Tsagerun Neja Delta sun yi barazanar kai hari Abuja da Lagos

Tsagerun Neja Delta sun yi barazanar kai hari Abuja da Lagos

- 'Yan ta'addan Neja sun yi ikirarin dawowa aikata manyan laifuka a yankinsu da babban birni

- 'Yan ta'addan sun bayyana cewa zasu kai mummunan hari jihar Legas da babban birnin tarayya

- Sun zargi gwamnatin tarayya da yin watsi da yankinsu tare da tura sojoji suna kashe mutanensu

'Yan ta'addan Neja-Delta, wadanda suka bar bindigoginsu sama da shekaru biyar, sun sake yin fito-na-fito inda suka yi barazanar sake daukarta su kai hari Lagos da Abuja.

Biranen biyu sune cibiyoyin kasuwanci da tafiyar da mulkin ƙasar, Daily Trust ta kawo.

'Yan ta'addan, a karkashin inuwar kungiyar Egbesu Liberation Fighters, a wani bidiyo da kafar yada labarai ta AIT ta yada ranar Talata, sun zargi gwamnatin tarayya da mayar da yankin saniyar ware tare da gazawa wajen aiwatar da shirin afuwar.

A cewar wani mamban kungiyar da ya rufe fuskarsa wanda bai ambaci sunansa ba, "Bayan amincewa da yarjejeniyar afuwar, har zuwa yau, babu makarantu, babu ruwan sha, babu haske, babu asibiti da hanyoyin shiga da mutanenmu za su more".

KU KARANTA: Kawai gwamnati ta kame Sheikh Gumi ta bincikeshi kan hada kai da 'yan bindiga, wasu 'yan Najeriya

Wata sabuwa: 'Yan ta'addan Neja Delta sun yi barazanar ruguza Abuja da Lagos
Wata sabuwa: 'Yan ta'addan Neja Delta sun yi barazanar ruguza Abuja da Lagos Hoto: BBC Hausa
Source: UGC

Kungiyar ta kuma koka da cewa "ba a samu ci gaba mai ma'ana ba" tare da aikin tsabtace Ogboni "saboda gwamnatin Najeriya ta yanke shawarar sanya siyasa a kan ci gaba mai ma'anar ga mutanenmu".

Ta nemi gwamnati da ta ba yankin damar gudanar da albarkatunsa "yadda ake gudanar da harkokin hakar gwal na Zamfara daga hannun mutanensu".

Ya kara da cewa, “A tsawon shekaru, mutanen Neja Delta sun yi ta kokarin ganin sun samar da yanayi mai kyau… amma babban abin takaicin mu shi ne, gwamnatin Nijeriya a tsawon wadannan shekaru ta yanke shawarar kula da lamuran yankin Neja Delta da safarar yara.

Ya bayyana cewa gwamnati ta ci amanar mutanen yankin tare da wulakanta 'yan yankin nasu.

"A maimakon haka, abin da ke bayyane shi ne kasancewar kwale-kwalen sojoji da dimbin sojojin da aka girke zuwa yankin Neja Delta wadanda ke kashewa, yi wa mata fyade, da nakasa marasa laifi na yankin."

KU KARANTA: El-Rufai: Najeriya ta fi kowace kasa a duniya yawan talakawa

A wani labarin, Wasu ‘yan bindiga da sanyin safiyar Talata sun afkawa karamar hukumar Matazu da ke cikin jihar Katsina inda suka yi garkuwa da Hajiya Rabi, surukar shahararren attajirin dan kasuwar nan, Alhaji Dahiru Barau Mangal.

Wata majiya daga danginsa, wacce ba ta so a bayyana sunan ta ba ta shaida wa jaridar Punch a Kano a wata hira ta wayar tarho cewa ‘yan bindigan wadanda suka iso garin da misalin karfe 1 na daren jiya.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Source: Legit.ng

Online view pixel