‘Yan garkuwa da mutane sun sace mata da dan malamin kwaleji a Zamfara

‘Yan garkuwa da mutane sun sace mata da dan malamin kwaleji a Zamfara

- Ana murna an rabu da Bukar ashe Habu na waje

- Duk da raguwar aiyukan ta’addanci a jihar Zamfara bayan jibge jami’an Sojoji, ‘yan garkuwa sun yi aikai-aika

- 'Yan bindigar sun yi awon gaba da iyalan wani malamin kwaleji

Masu garkuwa da mutane sun yi garkuwa da matan wani malamin kwalejin Ilimi ta Zamfara Alhaji Suleiman Abdullahi tare da ‘Dansa, a kauyen Gora Namayi dake karamar hukumar Maradun.

‘Yan garkuwa da mutane sun sace mata da dan malamin kwaleji a Zamfara
‘Yan garkuwa da mutane sun sace mata da dan malamin kwaleji a Zamfara

Wasu rahotanni sun bayyana cewa matan masu suna Suhaima Abdullahi da Adiza Abdullahi an yi garkuwa da su ne a dai-dai gurin da aka yi wani artabu da jami'an ‘yan sanda, inda jim kadan da barin kauyen aka yi garkuwa da matan.

KU KARANTA: Sojoji sun kashe wani gawurtaccen dan fashi da makami tare da kwato makamai (Hotuna)

Da yake tabbatar da faruwar al'amarin kwamishinan ‘yan sandan jihar ta Zamfara Kenneth Ebrimson, ya ce rundunar ‘yan sanda ta samu rahoton faruwar al'amarin, tare kuma da tura jami'an ‘yan sanda domin magance matsalar.

“Zamu yi wa al'umma karin bayani nan gaba kadan, domin mun aika da jami'an ‘yan sanda tawaga guda zuwa inda abin ya faru".

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel