Bidiyo: Yadda Likita Ya Manta da Burbushin Almakashi a Cikin wata Mata Yayin Tiyata

Bidiyo: Yadda Likita Ya Manta da Burbushin Almakashi a Cikin wata Mata Yayin Tiyata

  • A wani al'amari kamar almara, ana zargin wani likita ya manta da barbashin almakashi a cikin wata mata lokacin da ya yi mata tiyata
  • Matar mai suna Okoye Ogochukwu ta ce an yi mata tiyatar cire jariri a wani asibitin Legas, inda likitan ya manta da kayan aikin nasa
  • Ogochukwu ta koka cewa asibitin ya caje ta kimanin Naira miliyan 3, duk da cewa sun yi kuskure a tiyatar da suka yi mata har sau uku

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - Wata mahaifiyar ‘ya’ya uku da ke zaune a Legas mai suna Okoye Ogochukwu, ta nemi a yi mata adalci bayan ta fuskanci matsaloli daga tiyatar da aka yi mata a asibitin Faith City.

Kara karanta wannan

Gobara ta lakume sashen babban asibiti a Arewa, gwamna zai dauki mataki

Ogochukwu ta ce ta samu kumburi da matsalolin ciki sakamakon barbashin almakashi da suka bar mata a cikinta lokacin da aka yi mata tiyata a watan Mayun 2023.

Mai jego ta yi magana kan yadda likita ya manta da almakashi a cikinta
Legas: Likita ya manta da barbashin almakashi a cikin mai jego, ta nemi ayi adalci. Hoto: Owen Franken
Asali: Getty Images

An manta kayan tiyata a cikin mata

A wata tattaunawa ta musamman da jaridar The Punch, Ogochukwu ta ce cikinta ya fara kumbura sosai bayan wannan tiyatar, lamarin da ya sa ta koma asibitin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A lokacin da ta yi korafin, ta lura cewa, maimakon a dauki lamarin da gaske, likitanta, Ejim Chibike, ya yi ba'a game da halin da ta ke ciki, inda ya ce ta je ta rage kiba kawai.

Bayan wasu 'yan kwanaki, ta ce jikinta ya tsananta inda aka garzaya da ita asibitin, aka yi mata hoto wanda ya nuna cewa akwai barbashin kayan tiyata a cikinta.

Ogochukwu ta nemi adalci

Kara karanta wannan

An gaji: Lokuta 3 da jama'ar gari suka aukawa miyagun 'yan bindiga

A cikin faifan bidiyon hirar da aka yi da ita, Ogochukwu ta ce wani likita ya sake yi mata tiyata domin cire abin da aka manta, inda shi ma ya manta bai kwance wani dinki a cikin ba.

A haka dai rashin lafiya ta ci gaba da cin jikinta, har wurin da ba a dinke ba ya bude, yana zubar da wasu abubuwa daga cikin, inda aka sake garzayawa da ita asibiti.

Ogochukwu ta ce sai da aka yi mata tiyata a karo na uku, kuma asibitin ya caje ta kimanin Naira miliyan uku gaba daya. Lamarin da ta ce tana neman ayi mata adalci.

Ta ce:

"Sun azabtar da ni sosai, kuma sun ki su yi abin da ya dace. Ina neman su dawo mani da kudina da na kashe da kuma ba ni hakuri kan halin da suka jefa ni."

Kalli bidiyon matar a kasa:

Kara karanta wannan

Tsohon sanatan Arewa da ake zargin ya yi lalata da matar aure a bidiyo ya magantu

An manta tawul a wajen tiyata

A wani labarin, mun ruwaito cewa za a gurfanar da wasu likitoci biyu a gaban kuliya bayan da suka manta tawul a cikin wata mata da ya yi sanadin mutuwarta.

An ce Dakta Taiwo Shogunle da Dakta Adeleke Olusegun na aiki ne a garin Legas, inda suka gudanar da aikin tiyatar da ya kashe Omojola Bamgboye.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.