Likita ya manta da tawul a cikin wata mata.
–Likitoci biyu na wata asibitin kudi sun yi wani mantuwa mai daukan rai
–Sun manta da tawul a cikin tumbin Omojola Bamgboye
-Wannan sakaci ya kai ga ta rasa ranta.
–Am tsare likitocin guda biyu kuma an gurfanar da su.
Wani likitoci guda biyu zasu gurfana gaban Hukuma sanadiyar wata mantuwa mai hadarin bala'in da duka yi na manta da tawul a cikin tumbin mara lafiya bayan anyi mata aikin tiyata wanda shine sanadiyar bakuntan lahira da tayi.
Jaridar PM news ta bada rahoton cewa Dakta taiwo shogunle da dakta Adeleke Olusegun suna aiki ne a asibitin St. Raphael Divine Mercy Hospital da ke ijede, garin Ikorodun Jihar Legas inda suka gudanar da aikin tiyata akan aksn wata mata mai suna Omojola Bamgboye.
Bincike da yan sandan ofishin area 2 kwamand na unguwar onikan suka gudanar karkashin jagorancin sifeto Monday omoigui ne yasa aka damke likitocin An gurfanar da su a wata kotun majistare da ke igbosere akan cajin kisan kai.
KU KARANTA : Wasu Samari Sun Tsalleke Rijiya Da Baya
Lauyan jami'an yan sanda, Supol Rshiet ta fada ma kotu cewa likitocin cikin sakaci sun kashe omojola banlmgboye bayan sun manta da yawul a cikin ta . Ya ce laifin na bukatan azabtarwa karkashinsection 222(2) of the Criminal Law of Lagos State, 2011.
Amma likitocin sun musanta hakan kuma alkalin majistaren ya basu belin kudi N500,000 kowane daya da kudi kadara mai farashin kudin. An dakatar da karan zuwa ranan 9 ga watan satumba.
Asali: Legit.ng