Tashin Hankali Yayin da Aka Manta Kayan Aikin Tiyata a Cikin Wata Mata

Tashin Hankali Yayin da Aka Manta Kayan Aikin Tiyata a Cikin Wata Mata

  • Wani abu mai kama da almara ya afku da wata mata wacce ta dunga fama da ciwon ciki a kasar News Zealand
  • Likitoci sun gano wani abun tiyata da aka manta da shi a cikin matar lokacin da aka yi mata tiyatar haihuwa kimanin shekara daya da rabi da suka gabata
  • Tun bayan tiyatar haihuwar da aka yi mata, matar na ta fama da radadi a cikinta sannan tana ta yawon ganin likitoci daban daban

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Rahotanni sun kawo cewa likitoci sun manta da wani abun tiyata "da ya kai girman farantin cin abinci" a cikinta a wani asibiti da ke birnin Auckland a New Zealand.

Sashin Hausa na BBC ya rahoto cewa lamarin ya afku ne a wani asibiti da ke birnin Auckland a kasar News Zealand.

Kara karanta wannan

"Ba Za Ki Fito a Kowani Hoto Ba": Mai Hoto Ya Yanke Kanwar Amarya Daga Hotunan Biki Saboda Ta Ki Ba Shi Shinkafa

=

An manta abun tiyata a cikin wata
Tashin Hankali Yayin da Aka Manta Kayan Aikin Tiyata a Cikin Wata Mata Hoto: BBC Hausa
Asali: UGC

Likitoci sun cire kayan tiyatar da aka manta a cikin wata mata

An yi nasarar cire kayan tiyanar ne daga cikinta watanni 18 bayan ta haihu ta hanyar aiki, BBC News ta rahoto.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Matar ta sha fama da ciwon ciki tun bayan da aka yi mata miyata, inda ta dunga zaryar zuwa wajen likitoci daban-daban don gano abun da ke damunta.

Wasu yan rajin kare hakkin bil'adama sun ce asibitocin gwamnati basa mayar da hankali wajen kula marasa lafiya kamar yadda ya kamata.

An tattaro cewa ma'aikatar lafiya da ke lura da masu bukata ta musamman ta yi watsi da wannan al'amari a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin, 4 ga watan Satumba.

Sanarwar ta ce:

"Mutanen da suka yi wannan aikin tiyatar ba su iya yin bayani kan yadda suka manta da wannan abu a cikin cikinta ba, sannan ba su iya kai ga ganin abun ba a lokacin da suka kammala tiyatar."

Kara karanta wannan

Yadda Amarya Ta Fashe Da Kuka a Wajen Biki Bayan Masu Abinci Sun Ki Bayyana, Bidiyon Ya Yadu

Yadda likitoci suka gano tana mai rai a kwakwalwar wata mata

A wani labarin kuma, mun ji cewa wata kwararriyar likitar kwakwalwa, Dr Hari Priya Bandi, ta yi wa wata mata yar kasar Austalia mai shekaru 64 tiyata a kwakwalwa, inda ta yi gamo da abun da bata taba tsammani ba.

Dr Bandi ta fitar da wata tana mai rai wacce tsayinta ya kai santimita takwas wato inci 3 tana wulgawa a tsakanin almakashinta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel