'Na shafe tsawon shekaru 16 ina daukar ciki': Uwar Yara 12 Ta Bayyana Yadda aka yi Mata Tiyata Sau 6

'Na shafe tsawon shekaru 16 ina daukar ciki': Uwar Yara 12 Ta Bayyana Yadda aka yi Mata Tiyata Sau 6

  • Wata uwa mai shekaru 38 da yara 12, Iris Purnell, ta ce duk da cewar tana ta daukar ciki tsawon shekaru, tana son kari
  • Sai dai kuma matar ta bayyana cewa goyon ciki ba abu mai sauki bane domin sau shida ana mata tiyata
  • Matar ta yi suna sosai a shafin soshiyal midiya kasancewarta uwar ‘ya’ya da yawa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Wata mata mai suna Iris Purnell, ta shafe tsawon shekaru fiye da goma tana goyon ciki, kuma ta mallaki yara 12 a yanzu haka.

A hirarta da New York Post, matar ta bayyana cewa ta ji daban a yanzu da bata dauke da ciki kuma tana kokarin fuskantar zahiri.

Iyali
'Na shafe tsawon shekaru 16 ina daukar ciki': Uwar Yara 12 Ta Bayyana Yadda Ayi Mata Tiyata Sau 6 Hoto: New York Post, TikTok/Iris Purnell
Asali: UGC

Sau shida aka yi mun tiyatar haihuwa

Matar mai shekaru 38 ta bayyana cewa ta kan kasance tana daukar ciki duk shekara a tsakanin 2004 da 2019.

Kara karanta wannan

Matar Marigayi Alaafin Na Oyo Ta Dawo Daga Saudiyya Kawai Sai Ta Tarar Da Kyautar Mota Daga Wani Bawan Allah

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Matar wacce ke zaune a kasar Amurka ta kara da cewa za ta so kara samun ciki sau daya.

Idan ka zata goyon wadannan cikin na da sauki, ta ce:

“Ba duka cikina bane ke zuwa da sauki. An yi mun tiyata sau shida... amma goyon ciki na karawa ruhina karfi. Na koyi yin hakuri da zama da jikina.”

Tana da tarin mabiya a yanar gizo

Sai dai kuma, tuni aka daurewa matar mahaifa a matsayin hanyar yin tsarin iyali. Iris tana shafe tsawon lokaci wajen yin bidiyon iyali a shafinta na TikTok inda take farantawa mabiyanta.

Daya daga cikin bidiyonta wanda a ciki ta bayyana cewa ta shafe tsawon shekaru 16 a jere tana goyon ciki ya janyo cece-kucen da ke kasa:

Da Donn ya ce:

“Goyon ciki na tsawon shekaru 16 a jere hauka ne.”

Kara karanta wannan

Matar Aure Tayi Hayar Macen Da Za Ta Dinga Gamsar Da Mijinta, Ta Saka Mata Albashin N145K Duk Wata

nadinebrown420 ya ce:

“Toh sai da na dan dakata da bidiyon don kirga ranakun.”

Sassy6red ta ce:

“Hakan ya yi kyau amma babu manya da za su kula da kananan.”

KnotlessByKiara ta ce:

“Mahaifiyata mu 18 ta haifa kuma mun sha fama da rashin samun soyayya a lokacin da muke tasowa saboda ba Za ta iya bamu dukkanin abubuwan da muke bukata ba.”

Matashi Dan Shekara 27 Ya Koka Da Rashin Samun Aiki Saboda Ana Yi Masa Kallon Karamin Yaro

A wani labarin, wani dan kasar China, Mao Sheng, mai shekaru 27 ya bayyana matsalolin da yake fuskanta saboda kankantar halittarsa.

Mutumin wanda aka haifa kuma ya tashi a China, Mao Sheng ya kasance baida aikin yi saboda kankantar jikinsa.

Mao ya ce kamfanoni na kin karbarsa saboda basa so a alakanta su da bautar da karamin yaro saboda yanayinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel