Ajuri Ngelale, Lalong da Sauran Mutum 5 da Suka Ajiye Mukamai a Gwamnatin Tinubu
Abuja - Daga lokacin da Bola Ahmed Tinubu ya dare kujerar shugaban kasa a Mayun 2023, an samu wadanda suka yi murabus.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Wasu manyan jami’an gwamnatin Najeriya sun bar mukamansu domin rajin kansu, sun fadawa kowa cewa sun zabi su bar aiki.
Su wanene jami'an da suka bar gwamnatin Tinubu?
Legit ta jero wadanda suka rubutawa shugaban kasa takardar murabus kafin a kore su:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. Ahmed Rufai Abubakar
A watan Agustan 2024 ne Ahmed Rufai Abubakar ya zabi ya sauka daga matsayin shugaban hukumar leken asiri na kasa watau NIA.
Jim kadan bayan ya kai ziyara a fadar Aso Rock, Rufai Abubakar ya shaidawa duniya ya rubuta takardar murabus daga hukumar NIA.
Sanarwar ta ba da mamaki ganin cewa ba a saba jin mai rike da kujera ya sauka da kan sa ba sai dai wa’adinsa ya cika ko a tsige shi.
2. Yusuf Bichi
Wani kauli da aka samu daga Daily Nigerian ya bayyana cewa Yusuf Bichi ya bar kujerar shugaban DSS ne a sakamakon yin murabus.
Bichi wanda Muhammadu Buhari ya nada ya canji Matthew Seiyefa ya jagoranci hukumar tsaron na fararen kaya na shekaru har shida.
Bayan an tabbatar da saukar Bichi ne sai aka ji shugaban kasa ya nada sabon shugaban da zai rike ragamar hukumar DSS a Najeriya.
3. Abubakar Adamu Rasheed
A Yulin 2023 Farfesa Abubakar Adamu Rasheed ya zabi ya sauka daga kujerar shugaban hukumar NUC mai alhakin kula da duka jami’o’i.
Bayanan da aka samu a shafin NUC ya tabbatar da cewa Abubakar Adamu Rasheed ya hakura da kujerar ne domin ya koma jami’ar BUK.
Farfesan ya ce dama can ya na so ya bar ofishin, Muhammadu Buhari yana sauka aka nada Bola Tinubu sai ya ba da wuri a nadi wani.
4. Simon Lalong
Simon Lalong ya sauka daga kujerarsa ta Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, ya zabi ya zama Sanata mai wakiltar Filato ta Kudu.
Tsohon gwamnan ya tafi majalisar dattawa ne bayan nasarar APC a kotun karar zabe.
Ana da labari cewa a halin yanzu jihar Filato ba ta da wakilci a majalisar zartarwa (FEC) a sakamakon murabus da Sanata Simon Lalong ya yi.
5. Ajuri Ngelale
A safiyar Asabar aka samu labari cewa Hadimin Bola Tinubu a bangaren sadarwa, Ajuri Ngelale ya ajiye aiki yayin da shugaban kasar yake Sin.
Kamar yadda tashar NTA ta kawo labarin, Ngelale ya ba da uzuri da jinyar rashin lafiya, ya na mai fatan dawowa aiki da zarar an samu sauki.
Shugaban NUC ya yi murabus a gwamnati
Kwatsam rahoto ya zo cewa shugaban hukumar NUC na kasa, Abubakar Adamu Rasheed ya rubuta takardar ajiye aiki a gwamnati.
Kafin sabuwar gwamnati ta canza masu rike da mukamai, tsohon Shugaban Jami’ar ya tafi domin ya cigaba da koyarwa a jami'ar BUK.
Asali: Legit.ng