Masarautar Zazzau Ta Yi Rashi: Allah ya Yiwa Uwar Gidan Sarki Shehu Idris Rasuwa

Masarautar Zazzau Ta Yi Rashi: Allah ya Yiwa Uwar Gidan Sarki Shehu Idris Rasuwa

  • Allah ya yi wa Hajiya Habiba Shehu Idris rasuwa, uwar gidar marigayi Shehu Idris, sarkin masarautar Zazzau na 18
  • An ruwaito cewa Hajiya Habiba ta rasu ne a safiyar Juma'a, 30 ga watan Agustan 2024 bayan fama da 'yar gajeruwar jinya
  • Masarautar Zazzau ta yi karin haske kan lokacin jana'izar Hajiya Habiba, suruka ga Sarkin Zazzau, Ahmed Nuhu Bamalli

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Zariya, Kaduna - Rahoton da muka samu yanzu na nuni da cewa Allah ya yi wa Hajiya Habiba Shehu Idris rasuwa a ranar Juma'a, 30 ga watan Agustan 2024.

Hajiya Habiba ta kasance uwar gidar sarkin Zazzau na 18 daga tsatson Fulani, marigayi Alhaji Shehu Idris.

Kara karanta wannan

Tafiyar Kwankwasiyya ta samu matsala a Kano, fiye da mutane 6000 sun sauya sheka

Allah ya yiwa Hajiya Habiba Shehu Idris rasuwa, uwar gidan tsohon sarkin Zazzau
Zazzau: Allah ya karbi rayuwar uwar gidan Sarki Shehu Idris, Hajiya Habiba. Hoto: @Zazzau_Emirate
Asali: Twitter

Masarautar Zazzau ta rasa Habiba Shehu Idris

Masarautar Zazzau ce ta sanar da rasuwar Hajiya Habiba a shafinta na X a safiyar Juma'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Masarautar ta ce uwar gidar marigayi Dakta Shehu Idris ta rasu ne bayan ta yi fama da 'yar gajeruwar rashin lafiya.

Sarkin Zazzau ya yi rashin suruka

Sanarwar ta bayyana cewa marigayiya Hajiya Habiba ita ce mahaifiya ga Danruwata Babban Zazau, Alhaji Bello Shehu Idris.

Sauran manyan 'ya'yanta sun hada da Dan Isan Zazzau, Alhaji Umar Shehu Idris.

A cikin 'ya 'yan nata akwai Gimbiya Maryam Shehu Idris, matar sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, da sauransu.

An shirya jana'izar Hajiya

Kadan daga abin da sanarwar ta kunsa na cewa:

"Cikin mika lamura ga Allah, muna masu sanar da ku rasuwar Hajiya Habiba Shehu Idris a safiyar yau bayan ta yi fama da gajeruwar jinya.

Kara karanta wannan

Rai bakon duniya: Kwamishinan 'yan sanda a Najeriya ya riga mu gidan gaskiya

"Marigayiya Hajiya Habiba ita ce uwar gidan marigayi mai martaba sarkin Zazzau, Dakta Shehu Idris.
"Za a sanar da jama'a lokacin da za a gudanar da jana'izar Hajiya Habiba nan ba da jimawa ba."

Masarautar ta yi addu'ar Allah ya ji kan mai dakin marigayi sarkin Zazzau.

Sarkin Zazzau ya kwanta dama

A wani labarin a can baya, mun ruwaito cewa Allah ya yi wa sarkin Zazzau, Dakta Shehu Idris rasuwa yana da shekaru 84 a duniya.

An ce marigayi Sarki Shehu Idris ya rasu ne a asibitin 44 da ke Kaduna wajajen karfe 11 na safiyar Lahadi, 20 ga watan Satumban 2020.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.