Takaitaccen Tarihin Sarkin Zazzau na 18 Shehu Idris
Jaridar Rariya ta tsakura takaitaccen tarihin Sarkin Zazzau Shehu Idris daga littafin nan na kasar zazzau a jiya da yau. Mun dauko kadan daga ciki domin kawo maku takaitaccen tarihin na Shehu Idris.
An haifi Sarkin Zazzau wanda shi ne na 18 a jeringiyar Daular Fulani da ke Sarautar Kasar Zazzau a shekarar 1936. Mahaifin sa shi ne Malam Idrisu Auta wanda ‘Da ne wurin Sarkin Zazzau da aka yi daga Kasar Katsina watau Malam Sambo.
Shehu Idris yayi karantu ne a Makarantar Firamare ta Kofar Kuyambana da ke cikin Birnin Zazzau inda ya kammala a 1950. Daga nan kuma ya wuce Midil yak are a 1955. Bayan Midil Mai martaba ya tafi Makarnatar koyan Malanta ta Katsina.
A 1957 ne Shehu Idris ya kare Makarntar koyon malanta ya kuma fara aiki na N-A a matsayin Malamin Makaranta. Shehu Idris ya koyar a Makarantu da dama a Garuruwan Kasar Zazzau. Daga baya ne dai Shehu Idris ya ajiye aikin Malanta.
KU KARANTA: Kano ta yi wa Karuwai zafi a cikin watan Azumi
Mai martaba yayi kwas a Makarantar koyon aiki da ke Jami’ar Ahmadu Bello a Kongo inda bayan ya kammala a 1961 ya fara aiki a ofishin Sarkin Zazzau Aminu a matsayin Sakataren fadar Sarki. Daga nan kuma ya shiga Gwamnatin Kasar Arewa.
A 1967 ne Shehu Idris ya je Kasar waje inda bayan yayi wani kwas aka ba shi Hakimin Birni da kuma sarautar Dan Madami a 1973. Bayan rasuwar Sarki Aminu ne a wannan lokaci Shehu ya zama Sarki na 18 a Kasar Zazzau kuma daga gidan Katsinawa.
Yanzu dai shekaran Mai Martaba Sarki 43 a kan karagar mulki. Mai martaba ya dare kujerar Sarauta ne a 1975 lokacin bai kai shekaru 40 a Duniya ba. Mai martaba Shehu Idris yana da mata 4 da ‘Ya ‘ya da dama.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng