Hotunan yadda aka yi addu'ar ukun marigayi Sarki Zazzau, Alhaji Shehu Idris

- An yi addu'ar uku ta mai martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris a yau Laraba

- Babban basaraken ya rasu a ranar 20 ga watan Satumban 2020 bayan fama da yayi da gajeriyar rashin lafiya

- Dubban mutane sun yi tururuwar halartar sadakar ukun wacce aka yi safiyar Laraba

An yi addu'ar ukun rasuwar Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris a fadarsa da ke birnin Zaria a yau, 23 ga watan Satumban 2020.

Dubban jama'a da suka samu halarta sun hada da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai na jihar Kaduna.

Gwamnan jihar Kaduna, Muhammadu Badaru, ba a barsa a baya ba wurin zuwa addu'ar dattijon balaraben basaraken.

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mukhtar Ramalan Yero yana daga cikin wadanda suka halarci addu'ar ukun mai martaban a safiyar ranar Laraba.

Idan za mu tuna, a ranar Lahadi, 20 ga watan Satumban 2020 ne jama'ar birnin Zazzau da arewacin Najeriya suka samu labarin cewa Allah ya karba babban basaraken.

Alhaji Dakta Shehu Idris ya rasu yana da shekaru 84 a duniya.

Ya bar duniya yana da shekara 84 da haihuwa bayan fama da rashin lafiya.

Hotunan yadda aka yi addu'ar ukun marigayi Sarki Zazzau, Alhaji Shehu Idris
Hotunan yadda aka yi addu'ar ukun marigayi Sarki Zazzau, Alhaji Shehu Idris. Hoto daga Daily Trust
Source: Twitter

KU KARANTA: Yadda sama da 30m ta yi batan-dabo a ma'aikatar noma ta jihar Kano

Hotunan yadda aka yi addu'ar ukun marigayi Sarki Zazzau, Alhaji Shehu Idris
Hotunan yadda aka yi addu'ar ukun marigayi Sarki Zazzau, Alhaji Shehu Idris. Hoto daga Daily Trust
Source: Twitter

Hotunan yadda aka yi addu'ar ukun marigayi Sarki Zazzau, Alhaji Shehu Idris
Hotunan yadda aka yi addu'ar ukun marigayi Sarki Zazzau, Alhaji Shehu Idris. Hoto daga Daily Trust
Source: Twitter

KU KARANTA: Hotuna da tarihi: Manyan Sarakuna 8 da arewa ta rasa a cikin shekaru 20

Hotunan yadda aka yi addu'ar ukun marigayi Sarki Zazzau, Alhaji Shehu Idris
Hotunan yadda aka yi addu'ar ukun marigayi Sarki Zazzau, Alhaji Shehu Idris. Hoto daga Daily Trust
Source: Twitter

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel