Matashi Ya yi wa Yarinya Yar Shekaru 4 Yankan Rago, Ya Fadi Dalilin Kisan

Matashi Ya yi wa Yarinya Yar Shekaru 4 Yankan Rago, Ya Fadi Dalilin Kisan

  • Wani matashi mai shekaru 30 ya yi wa wata yarinya mai shekaru hudu yankan rago a jihar Enugu da ke Kudancin Najeriya
  • Rundunar yan sanda ta bayyana cewa mutumin da ya yanka yarinyar tana cikin barci a kan gado dan karamar hukumar Nsukka ne
  • Bayanai sun suna cewa mutumin yana zaune da iyayen yarinyar ne a gida daya kuma ya yi yunkurin kai hari a wasu a gidan

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Enugu - Rundunar yan sanda a jihar Enugu ta kama wani mutum da ake zargi da kisan wata yarinya mai shekaru 4 da haihuwa.

Rundunar yan sanda ta bayyana cewa mutumin ya yi amfani da wuka ne wajen yin kisan gilla ga yarinyar.

Kara karanta wannan

Bayan sarkin Gobir, an bayyana yadda yan bindiga suka harbe ɗan sarki

Enugu
Matashi ya yanka yarinya a Enugu. Hoto: Legit
Asali: Original

Jaridar Punch ta wallafa cewa yan sanda sun kama wukar da ake zargi mutumin ya yi amfani da ita da sauran abubuwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matashi ya yanka yarinya yar shekaru hudu

Rundunar yan sanda ta tabbatar da cewa ta kama wani matashi dan shekaru 30 da ake zargi ya yi yankan rago ga wata yarinya yar shekaru 4 a jihar Enugu.

Haka zalika rundunar ta bayyana cewa ta kama mutumin dauke da wuka, kayan shaye-shaye da kayan da ake zargi na tsafi ne.

Yadda matashi ya yanka yar shekaru hudu

Binciken yan sanda ya nuna cewa mutumin ya yi niyyar kai hari ga wani da suke cikin gida daya ne sai kuma ya samu yarinyar tana barci.

Daga nan ne kuma aka yi zargin cewa ya yi amfani da wuka ya yanka maƙogoron yarinyar kafin a je asibiti a samu ta rasu.

Kara karanta wannan

Sunayen gwamnonin Arewa da ake zargin sun kitsa zanga zangar adawa da Tinubu, Rahoto

Matashi ya amsa lafin yanka yarinya

Rahoton Channels Television ya nuna cewa matashin ya amsa laifin yi wa yarinyar yankar rago inda yace ya kashe ta ne alhalin yana cikin halin maye.

Kwamishinan yan sanda a jihar Enugu, CP Kanayo Uzuegbu ya tabbatar da cewa za a gurfanar da matashin a gaban kotu da zarar an gama bincike.

CP Kanayo Uzuegbu ya yi ta'aziyya ga iyayen yarinyar inda ta tabbatar musu da cewa za a yi adalci a binciken.

Makwabci ya sace yarinya a Bauchi

A wani rahoton, kun ji cewa wani mutumi mai suna Yawale ya sace diyar makwabcinsa a Bauchi kuma ya karbi kudin fansa.

An ruwaito cewa Yawale ya karbi kudin fansa daga wajen yan uwan yarinyar sannan ya birneta cikin gidansa a cikin garin Bauchi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng