A Bauchi, wani mutum ya yi garkuwa da diyar makwabcinsa kuma ya kasheta bayan karban kudin fansa

A Bauchi, wani mutum ya yi garkuwa da diyar makwabcinsa kuma ya kasheta bayan karban kudin fansa

  • Irin abinda ya faru a Kano, wani mutumi ya sace diyar makwabcinsa a Bauchi kuma ya karbi kudin fansa
  • Yawale ya bukaci kudin fansa amma bayan karba ya kashe yarinyar kuma ya birneta cikin gidansa
  • Jami'an hukumar tsaro sun damkeshi tare da abokinsa kuma zasu gurfana gaban kuliya

Toro, Bauchi - Jami'an tsaro sun damke wani mutumi mai suna Kabiru Abdullahi wanda ake zargi da kisan diyar makwabcinsa, Khadija yar shekara biyar a jihar Bauchi.

Kakakin hukumar Civil Defence na jihar, Garkuwa Adamu, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Litinin, rahoton ChannelsTV.

Ya yi bayanin cewa an damke Abdullahi ne tare da Alhaji Yawale kan zargin garkuwa da diyar Abdullahi Yusuf a Sabon Gari Narabi a karamar hukumar Toro.

Adamu yace:

"Bincike da aka fara sun nuna cewa Kabiru Abdullahi ya sace Khadika a gaban gidansu kuma ya shaketa ya jefata cikin buhu."

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Hadimin Buhari, Bashir Ahmad ya yi murabus daga kujerarsa

"Sai ya tuntubi mahaifinta Abdullahi Yusuf ya bukaci kudin fansa. Bayan tattaunawa, sun amince kan N150,000 don a saketa."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A Bauchi
A Bauchi, makwabci ya yi garkuwa da diyar makwabcinsa kuma ya kasheta bayan karban kudin fansa
Asali: UGC

A cewar Kakakin NSCDC, Yawale ya karbi N150,000 karkashin bishiyar tsamiya a garin Narabi.

Yace:

"Bincike ya kara nuna mana cewa an kashe Khadija ranar 27 ga Afrilu, 2022, kuma ya birneta dakin girkin abinci a gidansa."
"Masu bincike sun hako gawarta kuma sun kai asibitin Toro."

Budurwar Abdulmalik Tanko makashin Hanifa Abubakar ta ba da shaida a Kotu

A wani labari kuwa, masoyiyar Abdulmalik Tanko, shugaban makaranta da ake zargi da sace ɗalibarsa har ya kashe ta, Fatima Jibril, ta ce yaudararta ya yi ya sa ta cikin lamarin.

Aminiya Hausa ta rahoto cewa ta shaida wa Kotu cewa Tanko ya mata alƙawarin aure bisa haka ya umarci su sace Hanifa a makarantar Islamiyya.

Kara karanta wannan

Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, ya karbi Fom din takara kujerar Sanata

An gurfanar da Fatima tare da wani Hashim Iyaku a gaban Alkalin babbar Kotun jihar Kano, Mai Shari'a Usman Na'abba, domin kare kan su.

Da suke ba da shaida a gaban Kotun lokuta daban-daban, mutanen biyu sun ce Tanko ya yaudare su har ya kai ga jefa su cikin lamarin garkuwa da ƙaramar yarinyar.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel