Kano: Rundunar 'yan sanda ta kama saurayin da ya kashe 'yar shekara 8 bayan ya yi garkuwa da ita

Kano: Rundunar 'yan sanda ta kama saurayin da ya kashe 'yar shekara 8 bayan ya yi garkuwa da ita

- Matsalar garkuwa da mutane na cigaba da ci wa gwamnati da daidaikun jama'a tuwo a kwarya

- A kwanakin baya, Legit.ng Hausa ta wallafa rahoton yadda wani magidanci a Kano ya yi garkuwa da diyarsa tare da neman kudin fansa wurin matarsa

- Hakan ba ta dade da faruwa ba, sai ga shi yanzu an kara samun wani matashi da laifin kashe yarinya karama da ya yi garkuwa da it a Kano

Rundunar ƴan sanda reshen jihar Kano ta ƙwamushe wani saurayi mai shekaru 24 bisa zargin aikita laifin kisa da garkuwa da wata yariya ƴar shekara takwas, a cewar rahoton kamfanin dillancin labarai na ƙasa (NAN).

An daƙume saurayin mai suna Habibu Sale bisa zargin kashe Asiya Tasi'u a ƙauyen Chikawa da ke yankin ƙaramar hukumar Gabasawa bayan kuma ya amshe kuɗin fansa Naira ₦500,000 daga hannun iyayenta.

KARANTA: Arzikin gwal din Zamfara ba na gwamnati bane, in ji kwamishina Nuruddeen Isa

DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, mai magana da yawun rundunar ƴansandan jihar Kano, ya ce saurayin da ake zargin ya aikata laifin tun watan Yuni na shekarar 2020.

Kano: Rundunar 'yan sanda ta kama saurayin da ya kashe 'yar shekara 8 bayan ya yi garkuwa da ita
Kwamishinan rundunar 'yan sandan jihar Kano; A. H. Sani @Daily-trust
Asali: Twitter

Ya shaidawa NAN cewa binciken da aka gudanar ya nuna cewa ya binne gawar Asiya a wata maƙarbarta da ke bayan garin Chikawa bayan ya karɓi kuɗin fansa daga hannun iyayenta.

KARANTA: Babu mai iya kamani, aikin Allah nake yi; Shekau ya zolayi sojoji a sabon bidiyo

An kama matashin ne sanadiyyar bin diddiginsa da ƴansanda suka yi zuwa jihohin Jigawa, Abia, Kaduna, Katsina da Birnin Abuja, acewar Abdullahi Haruna Kiyawa.

Ko a kwanakin baya sai da rundunar 'yan sandan Kano ta kama tare da gurfanar da wani magidanci, Fahad Ali, bisa zarginsa da yin garkuwa da diyarsa, mai shekaru hudu, tare da neman N2m a matsayin kudin fansarta daga wurin matarsa, mahaifiyar yarinyar.

Bayan ya yi garkuwa da ita, ya kira matarsa tare da neman ta gaggauta biyan kudin fansa N2m ko kuma a kashe diyarta, kamar yadda Legit.ng Hausa ta rawaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel