An yi zargin Fulani Makiyaya Sun Kashe Wata Yarinya A Jihar Ogun

An yi zargin Fulani Makiyaya Sun Kashe Wata Yarinya A Jihar Ogun

- Ana zargin Fulani da yawan aikata laifuka makamancin wannan a yankin Yewa Na Jihar

- Wannan bashi ne na farko da aka samu aukuwar lamari irin wannan ba a yankin

- Yarinya Mai kananan shekaru ta rasa ranta

Wasu da ake zargin yan fulani makiyaya ne sun soke wata yarinya mai karancin shekaru har lahira a jihar Ogun.

Kisan mutanen da ba suji ba basu gani ba a yankin Yelwa na Ogun ba sabon abu bane kuma har yanzun ba'a kawo karshen lamarin ba.

Wannan wata yarinya ce karama da aka kashe ta da kuruciyar ta wanda wasu mutane da ake zargin fulani makiyaya ne dayi.

Rahoto ya bayyana cewa an kashe Elizabeth Pascal ranar Litinin a CAC Olorunda, yankin Moriwi dake karamar hukumar Imeko-Afon.

KARANTA ANAN: Masu kula da majinyata a asibiti sun tsunduma yajin aikin gargadi a Ondo

A wani rahoto da jaridar Dailtrust ta wallafa ya bayyana cewa, Yarinyar mai suna Elizabeth Pascal taje dibar ruwa ne amma a hanyarta ta dawo wa ta hadu da ajalinta a hannun wasu mutane wanda suka kashe ta.

Fulani Makiyaya Sun Kashe Wata Yarinya Har Lahira A Jihar Ogun
Fulani Makiyaya Sun Kashe Wata Yarinya Har Lahira A Jihar Ogun
Asali: Facebook

KARANTA ANAN: 2023: Kwankwaso ya jinjinawa Wike, ya ce ya shirya zama 'shugaban ƙasa'

Sarkin Iselu, Oba Akintunde Akinyemi ya tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Litinin da daddare.

Ya kuma bayyana wa wakilin Jaridar cewa suna zargin yan fulani makiyaya ne da kashe Pascal, wanda sune suke cigaba da cin karan su ba babbaka a yankin Yewa na Ogun lokaci zuwa lokaci.

Daga cikin bayanin shugaban yankin yace, lamarin ya faru ne da misalin karfe 3pm na yamma.

"Eh, hakane, Fulani makiyaya ne suka kashe ta a Imeko afan. Ta je debo ruwa, a hanyarta ta dawo wa ta hadu da Fulanin kuma suka kashe ta har lahira," yace.

Yawan kai hare hare a yankin na Yewa na cigaba da karuwa tsawon makwanni uku da suka wuce, duk kuwa da cewa gwamnatin jihar tayi kokarin tsayar da lamarin.

Don samun maslaha Gwamna Abiodun ya ziyarci yankin da abun ya shafa kuma yayi alkawarin kawo Jami'ai kota kwana domin shawo kan kashe kashen.

Amma gwamnan ya kara da cewa wadanda ke wannan aika aikar ba fulanin asali masu son zaman lafiya bane. Saidai a ziyarar da ya kaiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari, gwamnan yace an samu zaman lafiya a yankin da abubuwan suka shafa.

A wani labarin kuma Manoman albasa a jihar Kano sun fara shiga damuwa kan yajin aikin kai kaya Kudu.

Sun kuma bayyana cewa, farashin albasan ya nuna alamun tabarbarewar kasuwancin albasa a jihar.

Wannan ya haifar da hauhawar farashin kayayyakin masarufi a kudu amma a arewa, farashin na ta faduwa warwas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262