Sai da Aka Biya Kudin Fansa Ƴan Bindiga Suka Sako Ƴan Bautar Kasa? NYSC Ta Magantu

Sai da Aka Biya Kudin Fansa Ƴan Bindiga Suka Sako Ƴan Bautar Kasa? NYSC Ta Magantu

  • Hukumar matasa masu yiwa kasa hidima (NYSC) ta sanar da cewa an samu damar kubutar da 'yan bautar kasar da aka sace a Zamfara
  • A shekarar 2023 ne Legit Hausa ta ruwaito cewa 'yan bindiga sun yi garkuwa da 'yan bautar kasar su 8 a kan hanyar Funtua zuwa Gusau
  • Shugaban hukumar NYSC, Manjo Janar Yusha'u Ahmed ya bayyana cewa babu ko daya daga cikin matasan da aka biyawa kudin fansa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Shugaban hukumar kula da matasa masu yiwa kasa hidima (NYSC), Manjo Janar Yusha'u Ahmed, ya yi magana kan 'yan bautar kasa da aka sace a Zamfara.

Manjo Janar Yusha'u ya ce 'yan bautar kasar takwas da aka yi garkuwa da su a hanyar Funtua zuwa Gusau a jihar Zamfara a ranar 17 ga Agustan 2023 sun kubuta.

Kara karanta wannan

Edo 2024: Dan takarar gwamna ya shiga tashin hankali, 'yan bindiga na farautarsa

NYSC ta yi magana kan 'yan bautar kasa da aka sace a 2023
'Yan bautar kasar da aka sace a 2023 a Zamfara sun samu 'yanci. Hoto: @officialnyscng
Asali: Twitter

An hana 'yan NYSC tafiyar dare

A wata ganawa da manema labarai a Abuja, Manjo Janar Ahmed ya yabawa jami’an tsaro da suka taimaka wajen ceto matasan, inji rahoton Channels TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Manjo Janar Ahmed ya jaddada kudirin gwamnati na kyautata jin dadin jama’a da tsaron ‘yan matasa masu yiwa kasa hidima.

"Muna ci gaba da baiwa 'yan bautar kasa shawara da su daina tafiye-tafiye da daddare saboda hadarin da ke tattare da shi."

- Inji shugaban na NYSC.

"Ba a biya kudin fansa ba" - NYSC

Jaridar Tribune ta ruwaito shugaban NYSC ya ce an kubutar da wasu daga cikin wadanda aka sace tun a 2023, kuma ya ce an sako na karshe a ranar Alhamis 21 ga Agusta, 2024.

Ya dage kan cewa babu kudin fansa da aka biya domin kubutar da matasan, sannan ya kuma yabawa jami’an tsaro kan nasarar da suka samu na ceton.

Kara karanta wannan

DHQ: Sojoji sun hallaka ƴan ta'adda sama da 150, sun kama wasu 302 a Najeriya

Ko da yake ba a kama wani daga miyagun ba, amma jami’an tsaro sun ce an kashe shugaban ‘yan ta'addan, kuma a halin yanzu matasan na samun kulawar likitoci.

An sace 'yan bautar kasa a Zamfara

Tun da fari, mun ruwaito cewa wasu 'yan bindiga sun yi garkuwa da matasa masu yi wa ƙasa hidima (NYSC) 8 a kan hanyar Funtua zuwa Gusau a jihar Zamfara

Baki ɗaya 'yan bautar ƙasar da lamarin ya shafa suna cikin wata motar Bas AKTC kuma sun fito ne daga Uyo, jihar Akwa Ibom, suka shiga ta Sakkwato a hanyarsu ta zuwa Zamfara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.