'Yan bindiga sun sace 'yan bautar kasa guda hudu a jihar Katsina

'Yan bindiga sun sace 'yan bautar kasa guda hudu a jihar Katsina

- Wasu da ake tunanin masu garkuwa da mutane ne sun sace wasu 'yan bautar kasa guda hudu a kan hanyar Katsina

- Lamarin dai ya faru ne da misalin karfe 11:30 na dare a yayin da 'yan bautar kasar ke kan hanyar su ta zuwa jihar Zamfara

- Kakakin rundunar 'yan sada ya tabbatar da faruwar lamarin

Wasu masu yiwa kasa hidima guda hudu da suke kan hanyarsu ta zuwa jihar Zamfara domin gabatar da ayyukan da aka rarraba musu, sun gamu da ibtila'i a hanya yayin da aka sace su a kan hanyar Funtua dake jihar Katsina.

A yadda rahoto ya bayyana, wadanda lamarin ya shafa, maza guda uku da mace guda daya, da kuma wasu dalibai daga kwalejin Rufus Giwa sun dauki shatar motar daga Owo, jihar Ondo zuwa jihar ta Zamfara inda za su gabatar da bautar kasar.

Sai dai a lokacin da direban motar ta su ya shiga karamar hukumar Funtua dake jihar Katsina, wasu mutane dauke da makamai sun rufe hanyar su, inda kuma suka fara harbin motar su.

Yayin da direban motar da wasu daliban na cikin motar suka samu suka gudu, hudu daga cikin daliban sun shiga hannun masu garkuwa da mutanen, inda suka wuce da su wani wuri da har yanzu babu wanda ya san ina ne.

KU KARANTA: Idan mijina baya gamsar dani fita zanyi na nemi maza a titi - Juliet Njemanze

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar 'yan sandan Najeriya, DCP Frank Mba, ya ce:

"Gaskiya ne, an sace hudu daga cikin su da misalin karfe 11:30 na dare. Rundunar ta tura jami'anta domin kamo wadanda suka sace din domin ceto rayukan su. Rundunar tana samun nasara a kokarin da take na gano maboyan 'yan bindigar."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng