Yanzu-yanzu: Mun ceto yan bautar kasa 4 da aka sace a hanyar Gusau - Yan sanda

Yanzu-yanzu: Mun ceto yan bautar kasa 4 da aka sace a hanyar Gusau - Yan sanda

- Masu garkuwa da mutane ne sun sace wasu 'yan bautar kasa guda hudu a kan hanyar Katsina

- Kakakin rundunar 'yan sada ya tabbatar da faruwar lamarin kuma ya ce an cetosu tare wani mutm daya

Jamian hukumar yan sandan Najeriya sun samu nasarar ceto matasa masu bautar kasa hudu da masu garkuwa da mutane suka sace a ranar Litinin.

Kaakin hukumar yan sandan, DCP Frank Mba, ya bayyana hakan ne da daren nan a shafin sada zumuntar hukumar.

Yace "Dakarun hukumar yan sandan Najeriya a yai 11 ga maris 2020 sun ceto masu bautar kasa hudu da aka sace ranar 9 ga Maris a hanyar Funtua zuwa Gusau yayinda suka nufi sansanin yan bautar kasa dake Gusau, jihar Zamfara.

Yan bautar kasan sune Oladehin Paul, Ojo Temitope, Ojewale Elizabeth da Adenigbuyan Adegboyega kuma an mikasu da dirkatan hukumar NYSC na jihar Zamfara yayinda shi kuma Mohammed Ardo, wanda aka ceto tare da su an mikashi ga iyalansa."

Mun kawo muku rahoton cewa Wasu masu yiwa kasa hidima guda hudu da suke kan hanyarsu ta zuwa jihar Zamfara domin gabatar da ayyukan da aka rarraba musu, sun gamu da ibtila'i a hanya yayin da aka sace su a kan hanyar Funtua dake jihar Katsina.

A yadda rahoto ya bayyana, wadanda lamarin ya shafa, maza guda uku da mace guda daya, da kuma wasu dalibai daga kwalejin Rufus Giwa sun dauki shatar motar daga Owo, jihar Ondo zuwa jihar ta Zamfara inda za su gabatar da bautar kasar.

Sai dai a lokacin da direban motar ta su ya shiga karamar hukumar Funtua dake jihar Katsina, wasu mutane dauke da makamai sun rufe hanyar su, inda kuma suka fara harbin motar su.

Yayin da direban motar da wasu daliban na cikin motar suka samu suka gudu, hudu daga cikin daliban sun shiga hannun masu garkuwa da mutanen, inda suka wuce da su wani wuri da har yanzu babu wanda ya san ina ne.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng