Miyagu Sun Matsa da Sace Sarakuna, An Ɗauke Hakimi da Ɗiyarsa a Kaduna

Miyagu Sun Matsa da Sace Sarakuna, An Ɗauke Hakimi da Ɗiyarsa a Kaduna

  • Miyagu sun matsa ƙaimi wajen kai hari kan sarkunan Arewacin kasar nan, yayin da su ka kai farmaki Kaduna
  • Kungiyar mazauna Kaduna ta Kudu (SOKAPU) ta tabbatar da cewa an sace hakimin Gurzan Kurama, Yakubu Jadi
  • Shugaban SOKAPU ya ce haka kuma miyagun sun sace karin mutane shida a harin da su ka kai a daren Asabar

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna - Masu garkuwa da mutane sun kai hari kan mazauna yankin Gurzan Kurama a daren Asabar inda su ka ɗauke mutane da dama.

Kungiyar mazauna Kaduna ta Kudu (SOKAPU) da ta tabbatar da harin, ta bayyana cewa ƴan ta'addan sun sace karin mutane shida.

Kara karanta wannan

Sarkin Gobir: Dattawan Arewa sun yi martani kan lamarin, sun tura sako ga Sultan

Kaduna
Miyagu sun sake sace basarake a Kaduna Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa miyagun sun sace hakimin yankin, Yakubu Jadi da ɗiyarsa, sai Iliya Yakubu, Nehemiah Tanko da Thomas Tanko.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lamarin sace masu rike da sarautun gargajiya na kara kamari a yankin Arewa maso Yammacin kasar nan, Channels Television ta wallafa.

An nemi ceto basarake daga hannun miyagu

Jami'in kungiyar mazauna Kaduna ta Kudu (SOKAPU), Josiah Yusuf Abraks ya nemi daukin jami'an tsaron kasar nan wajen ceto hakimin Gurzan Kurama.

Josiah ya kara da cewa iyalai da yan uwan wadanda aka sace sun fada mawuyacin hali, kuma akwai bukatar cetonsu cikin gaggawa.

Bayan sace Basarake, an fara taka tsan-tsan

Kungiyar SOKAPU ta ce akwai bukatar jama'a su rika ɗari-ɗari da baƙin fuska da ke gewaye a yankinsu.

Kakakin SOKAPU, Josiah Yusuf Abraks ya shawarci mazauna yankin su rika sa ido sosai akan bakin fuska da ke shige da fice a yankin, domin daƙile ayyukan sace jama'a.

Kara karanta wannan

Magana ta ƙare, kotun koli ta yanke hukunci kan sahihancin zaɓen gwamnan APC

Miyagu sun sace matar basarake da yaranta

A baya mun ruwaito cewa miyagu sun kai hari kauyen Galadimawa da ke karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna inda su ka sace matar basaraken yankin da yaranta.

Da isar miyagun ƙauyen su ka fara harbe-harbe domin firgita jama'a, daga bisani su ka sace Fatima Aliyu da yaranta biyu, Abdullahi Aliyu da Kamal Aliyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.