Ana cikin Kukan Talauci: Najeriya Za Ta Samu Tallafin Naira Biliyan 42 daga Amurka
- Gwamnatin Amurka ta sanar da cewa ta ware $27m a matsayin tallafi domin taimakawa Najeriya wajen yakar matsalar jin kai
- An ce tallafin wani bangare na tallafin $536m da gwamnatin Amurka za ta ba kasashen kudancin hamada ta ofishin Uzra Zeya ba
- Jakadan Amurka a Najeriya, Richard Mills, ya tabbatar da hakan a wata sanarwa a ranar Talata sannan ya yi karin bayani a kai
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya sanar da cewa Najeriya za ta samu $27m (N42.9bn) a wani bangare na tallafin $536m da za ta ba kasashen kudancin hamada.
Kasashen kudancin hamada su ne kasashen da ke a yammacin Afrika, Afrika ta tsakiya, kudancin Afrika da kuma gabashin Afrika.
An samu bayanin hakan ne a cikin wata sanarwa da aka wallafa a shafin ofishin jakadancin Amurka a Najeriya na yanar gizo a ranar 20 ga Agusta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta ce wannan tallafin wani bangare ne na kudurin Amurka na ba da taimako ga mutane marasa galihu da kuma kasashe masu karbar baki.
Amurka za ta ba Najeriya tallafin $27m
Jakadan Amurka a Najeriya, Richard Mills, ya jaddada tasirin sabon tallafin da gwamnatin Amurka ke bayarwa yana mai cewa:
“Wannan tallafin zai kawo sauyi sosai a rayuwar wadanda ke da tsananin bukata a Najeriya da ma Nahiyar Afrika baki daya.”
Karkashin sakatariyar harkokin tsaron fararen hula, dimokuradiyy da kare hakkokin bil Adama, Uzra Zeya, a hukumance aka gabatar da cikakken shirin tallafin.
Sanarwar ta ce wannan tallafin ya kawo jimillar taimakon jin kai da Amurka ke bayarwa ga yankin kudancin hamada a shekarar 2024 zuwa kusan dala biliyan 3.7.
Hanyoyin da tallafin zai taimaki Najeriya
Taimakon na da nufin magance muhimman bukatu na mutane masu rauni da suka hada wadanda 'yan ta'adda suka dai daita, masu neman mafaka, ‘yan gudun hijira, marasa galihu, da sauran mutanen da rikici ya shafa.
Tallafin zai kuma taimaka wajen samar da mafita mai dorewa ta fuskar komawar 'yan gudun hijira zuwa muhallansu da kuma inganta sansanonin 'yan gudun hijira.
Za a ba da tallafin ne ga mabukata ta ofishin ma'aikatar jama'a, 'yan gudun hijira, da bakin haure na Amurka da hadin guiwar ofishin ayyukan jin kai na USAID.
Karanta cikakken bayanin a kan tallafin $27m anan:
Falasdinu: Amurka ta daina taimakawa Isra'ila
A wani labarin, mun ruwaito cewa Amurka ta dakatar da sayarwa Isra'ila da makamai biyo bayan ci gaba da kai hare hare a Zirin Gaza duk da shawarwari da aka ba ta.
Wannan shi ne karon farko da shugaban kasar Amurka, Joe Biden ya karya rantsuwar da ya yi na taimakawa Isra’ila wajen kaiwa Falasdinawa hari.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng