Akwai 'Yan gudun Hijira 34, 000 na kasar Kamaru a jihar Cross River - SEMA
A ranar Juma'ar da ta gabata ne cibiyar bayar da agaji na gaggawa reshen jihar Cross River ta bayyana cewa, akwai kimanin 'yan gudun hijira 34, 000 daga kasar Kamaru dake fake cikin kananan hukumomi shida a fadin jihar.
Shugaban hukumar John Inaku, shine ya bayyana hakan yayin ganawa da kamfanin dillancin labarai na Najeriya a babban birnin Calabar na jihar.
Mista Inaku ya bayyana cewa, musabbabin da ya haifar da wannan matsala shine rikici da tashin tashina dake afkuwa a kasar sakamakon neman kamfa jamhuriyyar Ambazonia da 'yan kudancin kasar suka bukata.
A yayin ganawar sa da kamfanin dillancin labarai Mista Inaku ya bayyana cewa, 'yan gudun hijirar dake neman mafaka na zazzaune cikin kananan hukumomi shida na jihar da suka hadar da; Obudu, Boki, Ikom, Etung, Akamkpa da kuma Obanliku.
Legit.ng ta fahimci cewa, a halin yanzu akwai 'yan gudun hijira 34, 000 a jihar ta Cross River inda tuni majalisar dinkin duniya ta yiwa 21, 000 rajista tare da hadin gwiwar hukumar gudun hijira ta kasa.
KARANTA KUMA: Saraki da wasu gwamnoni 3 na shirin sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP
Mista Inaku ya kara da cewa, gwamnatin jihar na iyaka bakin kokarin ta wajen tallafawa 'yan gudun hijirar.
Kazalika adadin su na kara hauhawa da gwamnatin za ta gaza wajen ci gaba da daukar nauyin su, inda ya nemi kungiyoyi da cibiyoyin jin kai akan su kawo nasu tallafin.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng