'Yan Bindiga: Ana cikin Tashin Hankali a Sokoto, Wa'adin Karbo Sarkin Gobir ya Kare
- Al'ummar Sokoto sun bayyana tashin hankalinsu yayin da wa'adin da 'yan bindiga suka diba na kai kudin fansar Sarkin Gobir ya kare
- Mazauna Gatawa da ke Sabon birni a jihar Sokoto sun nuna takaici kan yadda matsin rayuwa ya hanasu hada kudin karbo hakiminsu
- Idan ba a manta ba, a cikin wani faifan bidiyo da 'yan bindigar suka fitar, Sarkin Gobir ya ce wa'adin kai N50m domin karbo sa ya kare
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Sokoto - Mazauna Gatawa da ke a Sabon Birni, jihar Sokoto sun dukufa addu'a ta neman Allah ya dawo da hakiminsu, Isa Muhammad Bawa.
Kwanaki 23 kenan da 'yan bindiga suka yi garkuwa da Sarkin Gobir da dansa a hanyarsu ta komawa Sabon Birni.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa wa'adin da 'yan bindigar suka diba na kai N500m na kudin fansar basaraken ya kare tun ranar Laraba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wani faifan bidiyo da 'yan bindigar suka fitar a baya bayan nan, Sarkin Gobir ya roki gwamnatin Sokoto, 'yan uwa da abokan arziki su taimaka su karbo shi.
Sarkin Gobir ya nemi taimakon gwamnati
Dan majalisar dokokin jihar mai wakiltar Sabon Birni, Aminu Boza ya tabbatar da cewa mutumin da ke cikin faifan bidiyon hakimin Gatawa ne.
A cikin faifan bidiyon, mun ruwaito cewa Sarkin Gobir ya bayyana rashin jin dadinsa, yana mai cewa:
"Ina sanar da 'yan uwana, masu fatan alheri, abokai da shugabanni cewa yau (Laraba) ita ce ranar karshe, don haka idan suna son su taimake ni, to su yi hakan yanzu.
“Na rantse da Allah madaukakin sarki cewa ko su (’yan bindigan) sun gaji saboda su ma sun yi iya kokarinsu amma babu wani yunkuri daga gwamnati.
"Ina fatan samun taimakonsu (gwamnati) saboda na yi musu hidima kusan shekaru 45, a bangaren sarautar gargajiya."
Mutanen Gatawa sun dage da addu'a
An ruwaito cewa mazauna yankin, cikin tsananin damuwa da halin da hakimin Gatawa ke ciki, sun kasa zaune sun kasa tsaye.
Malam Mahe, wani mazaunin Gatawa, ya ce al’ummar garin sun tsunduma cikin addu’o’i, ganin cewa ba za su iya tara Naira miliyan 500 da masu garkuwa da mutane ke nema ba.
Mazaunin Gatawa ya ce 'yan fashin daji duk sun kwace dukiyarsu, wasu kuma sun lalata a hare-haren da suka sha kai masu, don haka ne ba su da kudin karbo basaraken.
Ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jiha da su kubutar da hakimin da iyalansa.
Kalli bidiyon basaraken a kasa:
'Yan bindiga sun sace Sarkin Gobir
Tun da fari, mun ruwaito cewa 'yan bindiga sun yi garkuwa da sarkin Gobir da dansa yayin da suke hanyar komawa gida a karamar hukumar Sabon Birni a Sokoto.
Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar, Ahmed Rufai ya tabbatar da faruwar lamarin, tare da bayyana matakin da rundunar ta dauka domin kwato basaraken.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng