'Yan bindiga sun sace hakimi a Kano

'Yan bindiga sun sace hakimi a Kano

Wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wanene ba, a ranar Litinin sun sace Alhaji Adam Muhammad Sarkin Yamma, Hakimin Karshi, a karamar hukumar Rogo a jihar Kano.

An gano cewar 'yan bindigan sun kutsa ne har cikin uwar ɗakan Yamma misalin ƙarfe 3 na dare kuma suka yi awon gaba da shi kamar yadda LIB ya ruwaito.

A cewar wani abokinsa, Auwal Mustapha Iman, har yanzu masu garkuwa da mutanen ba su tuntubi iyalansa ba a lokacin hada wannan rahoton.

"An sace abokina, Adam Muhammad Sarkin Yamma a daren jiya. 'Yan bindiga sun kutsa ɗakin matarsa misalin ƙarfe 3 na dare su ka yi awon gaba da shi a Karshi.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Sojoji sun kai sumame maboyar 'yan Boko Haram, sun ceto mutane

"Shi ne Hakimin Karshi a karamar hukumar Rogo da ke jihar Kano. Har yanzu ba su tuntubi kowa ba kuma dukkan wayoyinsa a kashe su ke tun bayan da ake sace shi.

"Don Allah ku yi masa addu'a. Ku kai wa jami'an tsaro mafi kusa da ku rahoton duk wani abu da ku ka ji a kansa. Da fatan Allah zai kubutar da shi kuma ya tona asirinsu. Amin."

'Yan bindiga sun yi sace hakimi a Kano
'Yan bindiga sun yi sace hakimi a Kano
Asali: Twitter

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel