Rana Ta 6: Yadda Zanga Zangar Nuna Kin Jinin Gwamnatin Tinubu Ke Gudana a Jihohin Najeriya

Rana Ta 6: Yadda Zanga Zangar Nuna Kin Jinin Gwamnatin Tinubu Ke Gudana a Jihohin Najeriya

Zanga-zangar nuna adawa da gwamnatin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ta shiga rana ta biyar a yau Litinin, 5 ga watan Agustan 2024.

Ana ci gaba da gudanar da zanga-zangar domin nuna adawa da halin ƙunci da matsin tattalin arziƙin da ake fama da shi a ƙasar nan.

Yadda zanga-zangar adawa da Tinubu ke gudana
'Yan Najeriya na ci gaba da gudanar da zanga-zanga Hoto: Pius Utomi Ekpei
Asali: Getty Images

Za mu ci gaba da kawo muku yadda ake gudanar da zanga-zangar a jihohin Najeriya.

Sojoji sun kashe wani yaro a Zariya

A unguwar Samaru da ke Zariya, Legit ta samu labarin jami’an tsaro sun hallaka wani yaro mai shekara 16 da haihuwa.

Legit ta samu labari cewa sojoji sun harba bindiga, harsashi ya shigo kofar gida har ya kashe Ismail Ahmad dazu da safe.

Abin ya faru ne da kimanin karfe 11:00 na safiyar Talata a layin Sarkin Pawa da ke Hayin Dogo.

A shafinsa na Facebook, wani Khalifa Ringim II ya wallafa hotunan gawar wannan yaro da ake shirin birnewa a halin yanzu.

An watsar da zanga-zanga a garuruwa

Rahotanni daga tashar Channels sun tabbatar da cewa an yi watsi da zanga-zangar da ake yi da aka duba tituna a safiyar ranar Talata

Daga cikin dalilan akwai dokar hana fita da aka rika kakabawa a garuruwa dabam-dabam a Najeriya saboda yadda lamarin ya cabe.

An yi fashe-fashe a Zariya

Legit Hausa ta samu labari dazu cewa ya canza a garin Zariya inda aka yi zanga-zanga cikin kwanciyar hankali a makon da ya gabata.

Bata-gari sun fasa shagunan ‘yan kasuwa a unguwar PZ da ke karamar hukumar Sabon Gari a Kaduna safiyar Litinin 5 ga watan Agusta.

Jami’an ‘yan sanda sun yi kokari wajen ganin lamarin ya lafa inda aka watsa borkonon tsohuwa kuma aka cafke wasu miyagun matasan.

Majiyoyi sun shaida mana cewa wadannan matasa sun nufi wata unguwar bayan barin PZ.

Zanga Zanga: Yan Sanda Su Tarwatsa Masu Ɗauke da Tutar Rasha

Zanga zanga ta barke a jihar Katsina yayin da al'umma da dama suka fito dauke da tutocin kasar Rasha suna ihun cewa yunwa za ta kashe su.

Sai dai Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa rundunar yan sanda ta tarwatsa matasan ta hanyar fesa musu borkonon tsohuwa.

Matasa sun fito zanga zanga a Katsina ne bayan kwana uku ba su fito kan tituna ba kuma ana ganin kalaman shugaban kasa na ranar Lahadi ne suka fusatasu.

Jami'an tsaro sun cafke masu zanga-zanga a Abuja

Jami'an tsaro sun tarwatsa masu zanga-zanga a yankin Karu da ke birnin tarayya Abuja.

Jaridar The Punch ta ce masu zanga-zangar sun fara taruwa ne lokacin da jami'an tsaro suka rufar musu inda suka cafke mutum uku.

Masu zanga-zanga sun fito a Legas

Wasu daga cikin masu zanga-zanga sun fito a Legas domin ci gaba da nuna adawa da halin yunwa da tsadar rayuwar da ake fama da ita a ƙasar nan.

Jaridar Daily Trust ta sanya bidiyon masu zanga-zangar a shafinta na X.

An tsaurara matakan tsaro a Legas

An jibge jami'an tsaro masu yawa a dandalin Gani Fawehinmi da ke Ojota a jihar Legas.

Jaridar Premium Times ta ce kwamishinan ƴan sandan jihar Legas, Adegoke Fayoade na daga cikin jami'an tsaron da ke wajen.

An sanya dokar hana fita a Plateau

Gwamnatin jihar Plateau ta sanya dokar hana fita ta sa'o'i 24 a birnin Jos da Bukuru.

Jaridar Leadership ta ce an sanya dokar ne biyo bayan wasu ɓata gari da suka ɓalle shaguna tare da sace dukiyoyi a birnin na Jos yayin zanga-zangar da ake gudanarwa.

Masu shirya zanga-zanga za su yi jawabi

Masu shirya zanga-zangar #Endbadgovernance a Najeriya za su yi taron manema labarai a ranar Litinin, 5 ga watan Agustan 2024.

Za a gudanar da taron ne a dandanlin Gani Fawehinmi Freedom Park da ke Ojota a jihar Legas.

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Omoyele Sowore ne ya bayyana hakan a shafinsa na X da safiyar ranar Litinin.

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.