'Yan Najeriya da Suka Kwashe Shekara 24 a Gidan Yari ba Tare da Laifi ba Sun Samu Tallafi

'Yan Najeriya da Suka Kwashe Shekara 24 a Gidan Yari ba Tare da Laifi ba Sun Samu Tallafi

  • Bayan shafe shekaru 24 a gidan yari kan zargin sun kashe wata mata, Ismail Lasisi da Lukman Adeyemi sun shaki iskar 'yanci
  • Jim kadan bayan fitowarsu, suka ba da labarin irin azabar da suka sha a hannun jami'an tsaro kan laifin da ba su aikata ba
  • Ganin halin da suka shiga, 'yan Najeriya sun tausayawa magidantan, inda suka hada masu tallafin N1m domin gina rayuwarsu

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

’Yan Najeriya masu kishin kasa sun bayar da gudunmuwar akalla Naira miliyan daya ga tsofaffin fursunoni Ismail Lasisi da Lukman Adeyemi.

Idan ba a manta ba, Isma'il da Lukman sun shafe shekaru 24 a gidan yari bisa zarginsu da kashe wata mata, zargin da aka gano ba gaskiya bane daga baya.

Kara karanta wannan

Abubuwa 7 da suka jawowa gwamnatin Tinubu zanga zanga bayan shekara 1

Ismail Lasisi da Lukman Adeyemi sun samu kyautar N1m bayan fitowa daga gidan yari
'Yan Najeriya sun ba magidanta da aka daure shekara 24 ba da laifi ba kyautar N1m. Hoto: punchmetro
Asali: Twitter

A wata tattaunawa mai ratsa zuciya da suka yi da jaridar The Punch, Isma'il da Lukman sun ba da labarin abin da ya faru da su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka kama Lukman da Ismail

Sun fara da cewa an kama su tare da tsare su bisa zargin kashe wata mata a watan Agusta 2000, an kuma yanke musu hukuncin kisa a 2009.

“A watan Agustan 2000, bayan mun dawo gida daga aiki tare da wani abokina Ismaila Lasisi, sai aka gaya mana cewa ‘yan sanda sun zo neman Ismaila, aka ce ya kai kansa ofishinsu.
“Nan da nan na yanke shawarar bin shi zuwa ofishin, inda aka kama mu gaba daya. An azabtar da mu kamar za mu mutukan zargin kashe matar da ban ma santa ba.

- Lukman ya shaidawa jaridar Vanguard.

'Yan Najeriya sun ba da tallafin N1m

Kara karanta wannan

Fargabar zanga zanga: Tinubu ya dawo biyan al'umma tallafi, an ci moriyar arzikin kasa

Tsofaffin fursunonin sun mika godiyarsu ga cibiyar jinkai da sasantawa ta CJMR, karkashin jagorancin Fasto Hezekiah Olujobi, wadda suka ce ta taimaka wajen fitar da su.

Bayan neman taimako domin sake gina rayuwarsu, an wallafa bayanan asusun Lasisi a shafukan sada zumunta, inda suka ya samu kyautar Naira miliyan 1.

Labarin wadannan magidanta ya dauki hankalin jama'a musamman yadda suka ce an azabtar da su har sai da suka amsa laifin da sam ba su aikata ba saboda a daina azabtar da su.

Kalli tattaunawar da aka yi da su a nan kasa:

Mutane 3 sun yi shekaru a magarkama

A wani labarin, mun ruwaito cewa wani mai shekaru 51, Eddie Bolden, ya kwashi garabasar biliyoyi bayan da ya shafe shekaru 22 a gidan yari bisa kuskure.

Ba wai Bolden ne kawai aka taba garkamewa a gidan yari bisa kuskure ba, mun tattaro akalla labarin mutane 3 da suka shafe shekaru a kurkuku kafin aka gano ba su da laifi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.