Yanzu yanzu: Hotunan bikin murnar yaye fursunoni 76 da suka kammala NCE na ta yawo a kafofin sada zumunta

Yanzu yanzu: Hotunan bikin murnar yaye fursunoni 76 da suka kammala NCE na ta yawo a kafofin sada zumunta

- A kokarin ilmantar da masu zaman kaso a wasu daga gidan yari a Najeriya, fursunoni na shiga makaranta

- Fursunonin an ruwaito sun share wa'adin karatun NCE a wata makaranta da ke Yewa

- A ranar Litinin, hotunan yaye daliban ya watsu a kafafen sada zumunta don murna

Fursunoni saba'in da shida na tsohuwar cibiyar kula da tsofaffin yara na Abeokuta, Ibara, jihar Ogun, sun kammala karatu daga kwalejin ilimi ta Yewa (YCCE), kamar yadda hukumar NCos ta watsa a shafinta na Facebook.

Hukumar Kula da Yan Gidan Yari ta Kasa (NCoS) ce ta bayyana hakan, inda ta ce wasu 18 sun shiga karatu cikin kwasa-kwasai daban-daban.

Mojeed Olaniran, mai kula da ma'aikatar NCoS a jihar Ogun, ya bukaci fursunonin da su yi amfani da damar da hukumar ta basu don zama 'yan kasa na gari.

KU KARANTA: Ku shirya jure tsadar man fetur, Ministan mai ga 'yan Najeriya

Yanzu yanzu: Hotunan bikin murnar yaye fursunoni 76 da suka kammala NCE na ta yawo a kafofin sada zumunta
Yanzu yanzu: Hotunan bikin murnar yaye fursunoni 76 da suka kammala NCE na ta yawo a kafofin sada zumunta Hoto: Nigerian Correctional Service
Asali: Facebook

A tuna a baya cewa fursunoni 40 na cibiyar sun kammala karatunsu daga kwalejin YCCE a shekarar 2019, yayin da wasu fursunoni 13 a shekarar 2018 suka shiga makarantar NOUN

Sannan wasu 64 kuma aka ba su takardar shaidar koyon sana’a a cikin shekarar guda bayan da suka kware a sana’o’in da suke so. Fursunoni 69 kuma sun sami nasarar kammala shirin NCE a cikin 2017.

Bugu da kari, fursunoni 50 a halin yanzu suna gudanar da karatun digiri a NOUN kuma a cikinsu har masu karatun digiri na biyu.

Cibiyar, tare da tallafin Asibitocin da Fannin jin Dadin Fursunoni (HPWI) da Kuta Art Community, Kungiyoyin da ba na gwamnati ba sun horar da fursunoni 32 kan sana'ar Adire, Kampala, Batik, rini da Splash.

Babban abin da ya faru a bikin shi ne gabatar da lambar girmamawa ga Kwanturolan NCos na jihar Ogun MOJEED OLABODE OLANIRAN da Oba Kabiyesi Osile Oke-Ona. An kuma ba da kyaututtuka na girmamawa na ilimi ga daliban da suka cancanta.

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari ta kashe N37bn a tallafin 'Survival Fund', in ji Osinbajo

A wani labarin, Hukumar kula da gidajen yari ta Najeriya ta ce wasu da aka gargame su 18 ne suka kammala karatun digiri daga jami'ar karatu daga gida ta National Open University ta Najeriya, BBC Hausa ta ruwaito.

A wata sanarwar da mai magana da yawun hukumar, Francis Enabore ya fitar a yau Alhamis ta ce tsararrun sun kammala jami'ar ne a fannonin karatu daban-daban.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.