Rayuwar kurkuku ta fiye mani, in ji Mallam Gambo wanda ya shafe shekaru 21 a gidan yari

Rayuwar kurkuku ta fiye mani, in ji Mallam Gambo wanda ya shafe shekaru 21 a gidan yari

- Wani mutum mai matsakaicin shekaru ya ce halin da ya tsinci kansa a kurkukun ya koya masa abubuwa da dama game da rayuwa

- Mutumin yace yayi karatun Alkur'ani da wasu adabin Addinin Musulunci yayin da yake kurkuku

- A cewarsa, rayuwa ta fi masa dadi yayin da yake kurkuku fiye da lokacin da ya samu ‘yanci

Wani fursuna da aka saki kwanan nan daga cibiyar gyara hali ta Katsina, Malam Gambo Mohammed, ya ba da labarin yadda ya kwashe shekaru 21 a gidan yari, yana mai cewa rayuwa ta fi masa a kurkuku fiye da lokacin da ya samu ‘yanci.

A wata hira ta musamman da jaridar Daily Trust, Mohammed ya ce ya girma ne a unguwar PRP Brigade da ke karamar hukumar Nasarawa ta jihar Kano.

KU KARANTA KUMA: 2023: Faston Najeriya ya bayar da bayani kan wanda zai gaji Buhari

Rayuwar kurkuku ta fiye mani, in ji Mallam Gambo wanda ya shafe shekaru 21 a gidan yari
Rayuwar kurkuku ta fiye mani, in ji Mallam Gambo wanda ya shafe shekaru 21 a gidan yari Hoto: Daily Trust.
Asali: UGC

Legit.ng ta tattaro cewa ya ce bayan Kammala karatunsa na sakandare, bai iya ci gaba da karatunsa ba, ya kara da cewa ya shiga kasuwancin kifi ne a yankin Galadima na Kasuwar Sabon Gari.

Da yake bayar da labarin yadda ya tsinci kansa a gidan yarin, ya ce yana wurin bikin aure a gidan makwabcinsa kuma sai aka samu rashin fahimta tsakanin matasan.

Ya ce an kashe mutum daya a wurin, yana mai cewa lokacin da 'yan sanda suka zo, sai aka kama shi duk da cewa shi ma ya ji rauni.

A cewarsa, bayan wani lokaci, sai aka kai shi kotu aka tura shi gidan yari.

Ya ce:

"Na share tsawon shekaru biyar ina jiran shari'a. Daga karshe dai, an same ni da laifin kisan kai kuma an yanke min hukuncin daurin rai da rai amma na yi shekara 21 a kurkuku. Na zauna a babban kurkukun Kurmawa da ke Kano daga baya na koma Kaduna kafin a mayar da ni Daura ta jihar Katsina. A cikin garin Daura ne na sake samun 'yanci na a lokacin da gwamnati ta rage cunkoso a kurkuku. "

Sai dai, Mohammed, ya ce rayuwa a kurkuku ba abu ne da mutum zai sowa ko da makiyinsa ba ne saboda dole ne ya hakura kuma ya mika wuya ga Allah gaba daya.

KU KARANTA KUMA: Pantami: Tsohon jakada Campbell ya magantu, ya bayyana dalilin da ya sa Amurka ta baiwa ministan biza

Ya bayyana cewa a lokacin da yake kurkuku, ya yi karatun Alkur'ani da sauran litattafan addinin Islama, ya kara da cewa a duk tsawon lokacin da ya sadaukar da rayuwarsa wajen neman ilimin addinin Musulunci saboda a koyaushe yana cikin masallaci.

Rayuwa bayan kurkuku?

Mutumin yace:

"Lokacin da na dawo gida, na fuskanci kalubale da yawa. Na farko, iyayena sun mutu kuma an sayar da gidanmu. 'Yan uwana mata sun yi amfani da kudin don cin abinci. Daga baya, na koma gidan yari. A wurina, rayuwar kurkuku ta fi abin da na sama a waje kyau saboda ina samun komai kyauta a kurkuku.

"Kwanaki, wata kungiya a karkashin Hajiya Fauziyya ta kawo min dauki har ma sun samo min mata. An yi auren makonni biyu da suka gabata. Sun biya min kudin haya, yanzu na yi aure cikin farin ciki. Abin da nake nema yanzu shi ne aiki."

A wani labarin, Kabir Dakata, wani ‘dan gwagwarmaya da ya jefa wa gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje tambaya a kan batun zargin karbar Dala ya na fuskantar barazana.

Malam Kabir Dakata ya bayyana cewa rayuwarsa ta na fuskantar barazana a halin yanzu. Dakata ya bayyana haka a wata sanarwa da ya yi shafin Facebook.

Jaridar Daily Nigerian ta ce Dakata ya na cikin manyan ‘yan adawar Mai girma Abdullahi Ganduje.

Asali: Legit.ng

Online view pixel