“Mutane 5 ne Ke Rike da Akalar Gwamnatin Tinubu,” Shugaban SDP Ya Ambaci Sunaye

“Mutane 5 ne Ke Rike da Akalar Gwamnatin Tinubu,” Shugaban SDP Ya Ambaci Sunaye

  • Shugaban jam'iyyar SDP na ƙasa, Shehu Gabam, ya lissafo wasu mutane biyar da ya dace a tuhuma idan gwamnatin Tinubu ta gaza
  • Shehu Gabam ya ce waɗannan mutanen su ne kusoshin da ke tafiyar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu a halin yanzu
  • Shugaban na SDP ya dage kan cewa Shugaba Tinubu ya sauka daga kan hanya, lamarin da ya jawo za ayi zanga-zanga a kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Shehu Gabam, shugaban jam'iyyar SDP, ya lissafo mutane biyar da ya dace a kama da laifi idan Shugaba Bola Tinubu ya gaza wurin gyara ƙasar nan.

Daga nan sai shugaban SDP ya nuna rashin gamsuwarsa game da yadda gwamnatin Shugaba Tinubu ke tafiyar da lamuranta, abin da yake ganin ya jawo ake shirin yin zanga-zanga.

Kara karanta wannan

Mai neman takaran shugaban kasa ya dora alhakin zanga zanga a kan Bola Tinubu

“Mutane 5 Ne Ke Rike da Akalar Gwamnatin Tinubu,” Shugaban SDP Ya Ambaci Sunaye
“Mutane 5 Ne Ke Rike da Akalar Gwamnatin Tinubu,” Shugaban SDP Ya Ambaci Sunaye. Hoto daga @officialABAT
Asali: Twitter

Shehu Gabam ya yi wannan iƙirarin ne yayin da ya bayyana a shirin Channels TV, inda ya bayyana cewa waɗannan mutane biyar ɗin su ne kusoshin fadar shugaban ƙasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan Najeriya sun fara sarewa da gwamnati

Da a ce akwai wata alamar nasara a gwamnatin Tinubu, Gabam ya ce da matasan Najeriya ba su yi kira da a yi zanga-zanga ba, kuma ya ce babu hadin kai a fadar shugaban kasa.

A mahangar Shehu Gabam, Shugaba Tinubu ba zai iya daidaita lamuran Najeriya shi kadai ba, don haka akwai buƙatar ministoci da sauran masu mukamai su yi aiki tare.

Ya jaddada cewa rashin samun isassun hanyoyin sadarwa da hadin kai tsakanin wadannan ministocin zai dagula lamuran gwamnatin Tinubu.

Mutane 5 za a dorawa laifin gazawar Tinubu

Shugaban SDP ya ce Femi Gbajabiamila ne jigon farko a fadar shugaban kasa, inda ya kara da cewa shugaban ma'aikatan ne za a fara dorawa alhaki idan har Shugaba Tinubu ya gaza.

Kara karanta wannan

A kara hakuri, tattalin arziki na dab da gyaruwa: Abin da Tinubu ya fadawa sarakuna

Gabam ya lissafo mai ba Shugaba Tinubu shawara kan tsaron ƙasa, Nuhu Ribadu, a matsayin na biyu da za a tuhuma da gazawar gwamnati mai ci a yanzu.

Sauran sun hada da sakataren gwamnatin tarayya, George Akume, sai na hudu shugaban ma'aikatan Najeriya da kuma na biyar ministan yada labarai, Mohammed Idris.

Kalli tattaunawar a nan kasa:

"Tattalin arziki zai gyaru" - Tinubu

A wani labari na daban, mun bayyana muku cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa tattalin arzikin Najeriya zai gyaru.

Ya amincewa kan cewa akwai yunwa da matsin rayuwa a ƙasar nan kamar yadda ya bayyanawa sarakunan gargajiya da ya gana da su.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.