Da Dumi-Dumi: Allah ya yi wa tsohon Ministan Kuɗi na Najeriya rasuwa

Da Dumi-Dumi: Allah ya yi wa tsohon Ministan Kuɗi na Najeriya rasuwa

  • Chu Okongwu, kwararre a bangaren tattalin arziki kuma tsohon ministan kudi a zamanin Ibrahim Badamasi Babangida, ya riga mu gidan gaskiya
  • Baya ga ministan kudi, Okongwu, ya rike mukamin ministan tsare-tsare na kasa, ministan man fetur da ministan harkokin yan fadar gwamnati
  • Okongwu wanda shine da na farko cikin yara takwas wurin iyayensa ya ce ya taba aiki a matsayin dan jarida a Daily Times

Chu Okongwu, kwararre a bangaren tattalin arziki kuma tsohon ministan kudi na Najeriya ya riga mu gidan gaskiya.

The Cable ta ruwaito cewa ya rasu ne a safiyar ranar Laraba, yana da shekaru 87 a duniya.

Da Dumi-Dumi: Allah ya yi wa tsohon Ministan Kuɗi na Najeriya rasuwa
Tsohon ministan kudi na Najeriya, Chu Okongwu, ya mutu. Hoto: The Cable
Asali: Facebook

An haifi Okongwu ne a ranar 23 ga watan Satumban 1934, a Jihar Anambra, Najeriya. Shi ne da na farko cikin 'ya'ya takwas wurin iyayensu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Makarantu da ayyuka da Okongwu ya yi

Ya yi karatu a St Michael's School, Aba daga 1941 zuwa 1946. Daga nan, ya tafi Kwallejin Gwamnati da ke Umuahia, inda ya yi karatu daga 1947 zuwa 1951.

Ya kuma yi karatu a bangaren tattalin arziki a Jami'ar Boston ya kammala digirinsa a 1961. Ya kuma yi karatu a Jami'ar Harvard daga 1961 zuwa 1965.

Ya yi aiki na shekaru takwas a karkashin gwamnatin Ibrahim Babangida, tsohon shugaban kasa na mulkin soja; da farko ya yi ministan kudi daga 1985 zuwa 1986, daga baya ya zama ministan tsare-tsare na kasa daga 1986 zuwa 1990. Daga baya ya yi ministan harkokin yan fadar gwamnati, daga bisani kuma ministan man fetur.

Rayuwa bayan an manyanta

A hirar da Vanguard ta yi da shi a 2013 yana da shekaru 79, Okongwu ya bayyana cewa 'yana da lafiya dai-dai da shekarunsa.'

Ya ce:

"Ina lallabawa ina tafiyar mile uku a kowanne rana; kwanaki hudu a sati, daga kai zuwa kafa, akwai matsaloli da ke zuwa da shekaru, amma ina tunanin ina farin ciki ina raye. Ba ni da shirin bata lokaci kan abubuwa marasa muhimmanci ... a duk minti da Allah ya bani a duniya. Na kan yi abu mai amfani."

Okongwu ya ce ya taba aiki matsayin dan jarida a Daily Times a matsayin sub-edita.

A watan Oktoba, yan bindiga sun cinna wa gidansa wuta a Jihar Anambra

Matar Shahararren Tsohon Gwamnan Najeriya Ta Rasu a Asibiti a Amurka

A wani labarin, Njideka Ezeife, matar tsohon gwamnan jihar Anambra wanda kuma dattijo ne a kasa, Chief Chukwuemeka Ezeife ta riga mu gidan gaskiya.

Njieka ta rasu ne bayan fama da gajeruwar rashin lafiya a wani asibiti da ke Amurka kamar yadda kungiyar dattawan Igbo ta sanar ta bakin sakatarenta Farfasa Charles Nwekeaku, The Sun ta ruwaito.

Nwekeaku ya ce ana sa ran tsohuwar matar gwamnan za ta dawo Najeriya ne a ranar Litinin, 13 ga watan Disamban 2021 amma kwatsam ta fara rashin lafiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel