"Rayuwa a Najeriya da Wahala", Malamin Addini ya Nanata wa Tinubu Halin da Kasa Ke Ciki
- Wani babban malamin addinin kirista, Bishof Stephen Fagbemi ya caccaki gwamnatin Bola Ahmed Tinubu kan halin da 'yan kasa ke ciki
- Malamin ya tura sako ga shugaban kan cewa 'yan Najeriya na takure a cikin halin matsi da rashin abin gudanar da rayuwarsu ta yau da kullum
- Bishof Rabaran Fagbemi ya ja kunnen gwamnatin tarayya kan matsalolin da rashin magance halin da ake ciki zai kara jefa kasar nan
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Ondo - Bishof a cocin Anglican Diocese da ke Owo a jihar Ondo, Rabaran Stephen Fagbemi ya bi jerin malaman addini da su ka fargar da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu halin da 'yan Najeriya ke ciki.
Rabaran Fagbemi ya yi kira ga shugaba Tinubu kan halin kunci, matsin tattalin arziki, rashin abin hannu da rashin tsaro da ya yi katutu a kasar nan.
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa malamin addinin ya yi kiran ne a taro na musamman karo na 14 da ya gudana a cocin St Stephen’s Church, Ipele a karamar hukumar Owo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An gargadi Tinubu kan karuwar rashin tsaro
Bishof Rabaran Stephen Fagbemi ya gargadi shugaba Bola Tinubu cewa akwai yiwuwar a samu karuwar ayyukan rashin tsaro a fadin kasa saboda rashin abin hannu.
Jaridar Nigerian Tribune ta wallafa malamin addinin na cewa yanzu zama a Najeriya na da wahalar gaske, shi ya sa mutane ke ta ficewa zuwa ketare domin neman mafaka.
Bishof Rabaran Fagbemi na ganin rashin magance matsalolin da 'yan kasar nan ke ciki zai jawo karuwar ayyukan ta'addancin da rashin tsaro.
Malamin addini ya caccaki Tinubu
A baya mun ruwaito cewa wani malamin addinin kirista, Primate Elijah Babatunde Ayodele ya ce tabbas shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya jefa 'yan Najeriya a cikin kunci da wahala.
Primate Ayodele wanda shi ne Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual Church ya kara da cewa matakan da gwamnatin Tinubu ta bijiro da su ne su ka kara jefa 'yan kasa matsi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng