'Yan Ta’adda Na Shirin Kai Hare Hare Kan Muhimman Gine Gine a Najeriya, Inji DHQ
- Hedikwatar tsaro (DHQ) ta ce dakarun sojojinta sun dakile shirin da ‘yan ta’adda ke yi na lalata muhimman kadarorin kasar nan
- DHQ ta ce dakarun da ke kula da wadandan muhimman kadarorin suna aiki ba dare ba rana domin dakile duk wani shirin ta'addanci
- Rundunar sojin ta sanar da hakan ne ta bakin daraktan yada labarai na tsaro, Manjo Janar Edward Buba a taron manema labarai
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Hedikwatar tsaro (DHQ) ta ce bayanan sirrinta sun bankado shirye-shiryen da wasu kungiyoyin ta'addanci ke yi na kai hari kan muhimman gine-ginen kasar nan.
Daraktan yada labarai na tsaro, Manjo Janar Edward Buba ne ya bayyana haka a lokacin da yake yiwa manema labarai karin haske kan ayyukan rundunar a ranar Alhamis a Abuja.
Sojoji sun dakile wani shirin kai farmaki
Buba ya ce tuni sojoji da hukumomin tsaro da ke da alhakin kare muhimman kadarorin kasar sun dauki matakan dakile hare-haren, in ji rahoton Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Manjo Janar Buba ya ce:
“Muna sane da wasu shirye-shirye na 'yan ta'adda na kaiwa wasu muhimman kadarorin kasar nan hari. Saboda haka, mun samar da matakan dakile irin wadannan hare-haren"
Buba ya yi kira ga ‘yan kasar da su marawa sojoji baya a yakin da suke da ‘yan ta’adda ta hanyar fallasa masu yin aiki da 'yan ta'addan da ke zaune a cikinsu.
"Dole mu yaki 'yan ta'adda" - Sojoji
Jaridar The Nation ta ruwaito daraktan yada labarai na hedikwatar tsaron ya ce wadannan ‘yan ta’addan makiyan Najeriya ne da ya kamata a yake su ta kowacce hanya.
Ya ce kusan kullum sai sojoji sun yi artabu da 'yan ta'adda wadanda kullum suke kokarin kashe ‘yan kasar ko suka riga da suka yi kisan.
“A wannan fadan, akwai bukatar ‘yan kasa su fahimci cewa, ba za mu taba yin kasa a gwiwa ba a kan tsaro, idan kuwa muka nuna sarewa, to za matsalar tsaron za ta shafi kowa."
- A cewar Manjo Janar Buba.
Sojoji sun halaka 'yan ta'adda 150
A wani labarin, mun ruwaito cewa dakarun sojojin Najeriya sun halaka ƴan bindiga 188 tare da kama wasu 330 a cikin makon da ya gabata a Arewacin ƙasar nan.
Kakakin hedikwatar tsaro ta DHQ, Manjo Janar Edward Buba, ya ce ga dukkan alamu sojoji sun kamo hanyar kawo ƙarshen duk wani nau'in ta'addanci.
Asali: Legit.ng