Bashin Naira Tiriliyan 37: Gwamnan CBN Ya Fadi Ainihin Abin da Ya Jawo Tsadar Abinci

Bashin Naira Tiriliyan 37: Gwamnan CBN Ya Fadi Ainihin Abin da Ya Jawo Tsadar Abinci

  • Gwamnan bankin Najeriya (CBN), Yemi Cardoso, ya danganta tsadar kayayyaki da bashin Naira tiriliyan 37.5 da aka baiwa gwamnatin tarayya
  • A ranar 23 ga Mayu, 2023, majalisar dattijai ta amince da bashin 'Ways and Means' na Naira Tiriliyan 30 bisa bukatar Muhammadu Buhari
  • Mista Cardoso ya ce dole ne 'yan Najeriya su girbi abin da ke tare da karbar wannan bashin, yayin da ya ke bayyana matakan daidaita tattalin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Olayemi Cardoso, gwamnan CBN, ya ce Najeriya na fuskantar hauhawar farashin kayayyaki sakamakon bashin Naira Tiriliyan 27 na 'Ways and Means' da ta karbo.

A ranar 23 ga Mayu, 2023, majalisar dattijai ta amince da bashin 'Ways and Means' na Naira Tiriliyan 37.5 kamar yadda tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukata a lokacin.

Kara karanta wannan

Wayas: Gawar tsohon shugaban majalisar dattawa da ya mutu a Landan ta iso Najeriya

Gwamnan CBN ya yi magana kan hauhawar farashin kayayyaki
Gwamnan CBN, Yemi Cardoso ya fadi abin da ya jawo tsadar kayayyaki. Hoto: @cenbank
Asali: Facebook

CBN ya fadi dalilin tsadar kayayyaki

Da yake magana a ranar Alhamis a wani taron Businessday, Mista Cardoso ya ce an kuma samu hauhawar farashin sakamakon kudaden da ke yawo sun yi yawa, inji rahoton The Cable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan bankin na CBN ya ce a yanzu Najeriya na girbar abin da ta shuka ne na karbo tulin bashi, wanda ya haifar da matsala ga tattalin arziki.

“Dukkanmu mun ga yadda bashin 'Ways and Means' ya haura zuwa N27trn kuma wani lamunin na N10.5trn. Dole bashin zai zo da matsala. A yanzu muna girbar sakamakon karbo bashin."

- A cewar Cardoso.

Tsawwala kudin ruwa da MPC yayi

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa a cikin watan Mayu, kwamitin tsare-tsare na kudi (MPC) na CBN ya kara kudin ruwa daga kashi 24.75 zuwa kashi 26.25.

Kara karanta wannan

Wahalar fetur ta tsananta a Najeriya, NNPC zai nemo sabon rancen dala biliyan 2

A cewar gwamnan CBN, kwamitin MPC bai manta da cewa kasar na bukatar bunkasar tattalin arziki a lokacin karin kudin ruwan ba.

Sai dai Mista Cardoso ya ce wannan hauhawar farashin kayayyakin na dan lokaci ne domin kwamitin MPC na yin duk mai yiwuwa domin daidaita tattali da darajar Naira.

CBN ya dakatar da ba gwamnati bashi

A wani labarin, mun ruwaito cewa babban bankin Najeriya ya ce daga yanzu ba zai kara ba gwamnatin tarayya bashin kudi a tsarin lamuni na 'Ways and Means' ba.

Gwamnan babban bankin, Olayemi Cardoso ya ce har yanzu babban bankin na bin gwamnti bashin naira tiriliyan 4.36 wanda ya saba wasu dokokin CBN.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.