Kano: Sadakar N100,000 Ya Saka Magidanci Sake Matarsa a Gadon Asibiti
- Auren wata matashiya ya mutu murus saboda an hana mijinta kudin sadaka da aka bata a asibiti a jihar Kano
- Tun da fari dai an kai matar asibitin Waziri Gidado a Kano haihuwa, wacce ta zo da matsalar jijjiga yayin nakuda
- Amma rahotanni sun ce kullum sai uwar matar ta yi kukan rashin kudin asibiti, sai kwatsam aka ba su sadaka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. Jihar Kano- Yayin da ake fafutukar ganin jama'a a Kano sun dauki aure da daraja, sai ga wani magidanci ya saki matarsa a gadon asibiti. Labarin sakin ya dauko asali ne saboda hana shi wani kaso na sadakar N100,000 da aka bawa matarsa.
Wannan na kunshe cikin labarin da mai bawa gwamna Abba Kabir Yusuf shawara kan jin kai, Fauziyya D Sulaiman ta wallafa a shafinta na Facebook.
Magidanci ya nemi a raba sadaka
Wani magidanci da matarsa ta je haihuwa asibitin Waziri Gidado ya nemi lallai sai an raba sadakar N100,000 da aka bawa matarsa an ba shi N50,000.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahotanni sun ce an kai matashiyar ta na jijjiga, kuma ko sisi mai gidan bai ajiye a matsayin kudin magani ba.
Kwatsam sai masu bayar da taimako su ka bi ta asibitin, inda matar da mahaifiyarta ke jinya ta samu sadakar N100,000 kamar sauran majijyata a asibitin.
Mahaifiyar mata ta hana sadaka
An ce bayan mahaifiyar mai jego ta karbi sadakar ne ta godewa Allah saboda sun samu saukin kudin magani.
Rahotanni sun ce duk lokacin da aka rubuta masu kudin magani sai uwar ta yi kuka saboda ba su da shi.
Amma ana samun sadakar sai mijin 'yarta ya zo ya ce sai an ba shi hakkinsa tunda matarsa aka bawa sadaka, ita kuma uwar mata ta ce ba za ta bayar ba.
Miji ya saki matarsa saboda sadaka
Bayan an hana magidanci wani kaso na kudin sadakar da ake biyawa matarsa mai jijjiga kudin asibiti sai ya fusata.
Saboda haka ya je ya taho da yayansa a kan lallai sai an ƙwato masa hakkinsa, lamarin da uwar mata ta ce a bari idan an sallame su, kudi ya yi saura sai a ba shi.
Amma daga bisani mijin ya dauki mataki, inda a dakin asibiti, ya saki matar;
"Tun da an hana ni hakkina a cikin kudin to ki je na sake ki, sai uwar ta ki ta ci gaba da rike ki."
Kano: Ma'aurata sun sace matashiya
A wani labarin kun ji cewa wasu ma'aurata sun shiga hannun hukuma bisa zargin sace matashiya a Kano.
Ana zargin Mista da Misis Mathew Auta mazauna Nomansland da ke Sabon Gari a karamar hukumar Fagge da laifin satar mutum.
Asali: Legit.ng