Yan Bindiga Sun Gwabza Fada, Hatsabibin Mai Garkuwa da Mutane Ya Sheka Lahira
- Rundunar sojin Najeriya ta kai farmaki kan yan bindiga a wasu ƙananan hukumomin jihar Taraba a Arewa maso gabas
- Wani gawurtaccen mai garkuwa da mutane ya sheka lahira a karamar hukumar Wukari bayan sun yi fada a tsakaninsu
- Haka zalika rundunar sojin ta yi nasarar ƙubutar da wasu mata da yan bindiga suka yi garkuwa da su a garin Lau
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Taraba - Dakarun sojin Najeriya sun kai jerin hare haren kan yan bindiga a wasu yankunan jihar Taraba.
Rundunar sojin ta samu nasarar ƙubutar da wadanda aka sace da kama wasu masu garkuwa da mutane.
Wani mai garkuwa da mutane ya sheka lahira yayin da fada ya kaure a tsakaninsu kamar yadda rundunar sojin ta wallafa a shafin Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Fada ya kaure tsakanin yan bindiga
Bayan jin karar harbe harbe a yankin Chinkai a garin Wukari, rundunar sojin Najeriya ta yi gaggawar isa wajen.
Da zuwan sojojin suka samu yan bindiga ne suka yi mummunan fada a tsakaninsu kuma sun samu wani dan bindiga mai suna Alhaji Gana kwance cikin jini.
Alhaji Gana yana cikin miyagun yan bindiga da ake nema ruwa a jallo kuma ya fitini jihar Taraba da ayyukan barna.
Sojoji sun ceto mutane a Lau
A ranar 8 ga watan Yuli sojojin Najeriya suka kai farmaki kan maboyar yan bindiga a dutsen Adamu Katibu a karamar hukumar Lau.
Farmakin ya jawo nasarar kama masu garkuwa da mutane uku da ceto wasu mata biyu da suka kama.
A ranar 7 ga watan Yuli yan bindigar suka sace matan, Asma'u da Hauwa'u kuma an mika su ga iyalansu bayan duba lafiyarsu a asibiti.
Yan bindiga sun yi fada a Zamfara
A wani rahoton, kun ji cewa an gwaba ƙazamin faɗa a tsakanin ƙungiyoyin ƴan bindiga uku a jihar Zamfara wanda ya jawo aka samu asarar rayuka masu yawa.
A mummunan artabun dai an hallaka shugabannin ƴan bindiga biyu, Kachallah Gwande da Ƙachallah Madagwal tare da mayaƙa mutum 12.
Asali: Legit.ng