An Zargi Sarki da Kwace Gonakin Talakawa, Ya Bayyana Gaskiyar Lamarin

An Zargi Sarki da Kwace Gonakin Talakawa, Ya Bayyana Gaskiyar Lamarin

  • Mai martaba sarkin Muri, Alhaji Abbas Njidda Tafida ya wanke kansa daga zargin da ake masa na kwace gonakin mutanen garin Kachalla
  • Alhaji Abbas Njidda Tafida ya ce a matsayinsa na uban kasa zai kare hakkin mutane a ko da yaushe ba tare da nuna wariya ba
  • Shugaban kungiyar cigaban ƙabilar Mumuye na kasa, Ezekiel Augustine ne ya zargi sarkin Muri da kwace gonakin yan kabilarsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Taraba - Sarkin Muri, Alhaji Abbas Njidda Tafida ya bayyana gaskiya kan zarginsa da aka yi da kwace gonaki.

Sarkin ya bayyana cewa shi uban kasa ne da yake tallafawa al'umma domin su samu hanyar dogaro da kai.

Kara karanta wannan

Gina layin dogo: Ana fama da matsin tattali, Tinubu zai karbo sabon bashi daga China

Taraba
Sarkin Muri ya yi magana kan zargin kwace gonaki. Hoto: Legit
Asali: Original

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa shugaban kungiyar yan kabilar Mumuye, Ezekiel Augustine ne ya zargi sarkin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zargin da aka yiwa Sarkin Muri

Ezekiel Augustine ya zargi sarkin Muri, mai martaba Abbas Njidda Tafida da kwacewa da lalata gonakin yan kabilarsa.

Saboda haka Ezekiel ya yi kira ga gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas ya dauki mataki kan sarkin domin kwato musu hakkinsu.

Kwace gonaki: Martanin sarkin Muri

Alhaji Abbas Njidda Tafida ya bayyana cewa shi ya ba yan ƙabilar Mumuye aron gonaki su rika nomawa a yankin, rahoton Daily Post.

Ya kuma dauki yan jarida sun zagaya gonakin domin duba ko an lalata shukar da suka yi kamar yadda Ezekiel ya zarge shi.

Mutanen Kachalla sun yi shaida

Yayin zantawa da dattawan garin Kachalla, sun tabbatarwa yan jarida cewa sarkin ya saye gonakin daga yan kabilar Mumuye shekaru 25 da suka gabata.

Kara karanta wannan

"Tuna halacci ke hana ni ɗaukar wasu matakai": Gwamna ga mai gidansa

Dattawan sun yi kira ga matasan yankin kan su yi taka tsantsan da marasa son zaman lafiya da ke son tayar da fitina a yankin.

Bauchi: An zargi basarake da kwace gonaki

A wani rahoton, kun ji cewa al'ummar kauyen Tulu da ke yankin Lame ta karamar hukumar Toro ta jihar Bauchi sun koka a kan fin karfin da mai unguwar Tulu yake masu

Mazauna yankin Tulu sun zargi mai anguwar da hakimin kauyen da hada kai wajen kwace masu gonaki da filayensu sannan su siyar wa wasu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng