Rikicin Zamfara: Jaji ya gargadi Gwamna Matawalle a kan kwace gonaki
Tsohon ‘dan majalisar tarayya na jihar Zamfara, Honarabul Aminu Sani Jaji, ya yi magana game da shirin gwamnati na maida filayen jama’a a karkashin hannunta.
Aminu Sani Jaji ya ja-kunnen Bello Matawalle da cewa ya guji karbe gonakin da jama’a su ka mallaka, kamar yadda ake rade-radin cewa gwamnatinsa za ta yi.
Hon. Aminu Jaji ya bayyana cewa muddin gwamna Bello Matawalle bai janye wannan mataki da ya dauka ba, zai iya maka shi a gaban kotu domin ya nemi hakkinsa.
Aminu Jaji wanda ya rike shugaban kwamitin tsaron kasa a majalisar wakilai, ya ce karbe filayen da jama’a su ka mallaka, keta hakkinsu ne wanda kuma ba zai dauka ba.
KU KARANTA: Idan ta kama za mu binciki gwamnatin baya – Gwamnan Imo
Mai girma Gwamnan Zamfara ta bakin Darekta Janar na hulda da jama’a a jihar, ya ce gwamnati za ta dawo da duk filayen da aka raba a kan wuraren kiwo karkashinta.
A wani jawabi da ya fitar a makon jiya, Jigon jam’iyyar APC a jihar Zamfara ya nuna cewa ba za su dauki matakin da sabon gwamnatin PDP ta ke neman dauka da wasa ba.
A cewarsa, kokarin ganin bayan ‘yan adawa da neman taso su a gaba ya sa gwamnatin Matawalle ta ke shirin karbe filayen da jama’a su ka mallaka tun 1999.
Jaji ya wakilci Mazabar Kauran Namado da Birnin Magaji a majalisar wakilai, kuma ya na cikin manyan wadanda su ka nemi takarar gwamnan jihar a karkashin APC.
Bello Matawalle, a kokarin da ya ke yi na kawo zaman lafiya a jihar ta Zamfara da Miyagu su ka sa a gaba, ya ce zai karbe duk wata gona da ke kan hanyar wurin kiwo.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng