Gwamnan Katsina Ya Haɗa Kai da SMEDAN, Ƙananun Ƴan Kasuwa Za Su Samu Bashin N1bn

Gwamnan Katsina Ya Haɗa Kai da SMEDAN, Ƙananun Ƴan Kasuwa Za Su Samu Bashin N1bn

  • An kulla wata yarjejeniya tsakanin gwamnatin jihar Katsina da hukumar SMEDAN domin ba kananun 'yan kasuwa tallafin kudi
  • An ruwaito cewa gwamnatin Katsina da SMEDAN za su hada N500,000 kowanne domin ba da rancen N1bn ga 'yan kasuwar jihar
  • Hadakar hukumar KASEDA da SMEDAN na daga cikin shirin 'MFP', wanda haɗin gwiwa ne tsakanin cibiyoyin kuɗi da jihar Katsina

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Gwamnatin jihar Katsina ta hada gwiwa da hukumar SMEDAN domin bayar da lamunin Naira biliyan 1 ga kananan ‘yan kasuwa a jihar.

Gwamnatin Katsina ta nemi wannan lamun ne ta hannun hukumarta ta bunkasa sana’o’i (KASEDA), wanda ke dauke da rangwamen kudin ruwa.

Kara karanta wannan

Najeriya za ta samu bashin $150bn da halatta auren jinsi a yarjejeniyar Samoa?

Gwamnatin Katsina da hukumar SMEDAN sun kulla yarjejeniyar kudi
Gwamnatin Katsina za ta ba kananun 'yan kasuwa tallafin N1bn tare da hadin guiwar SMEDAN. Hoto: @Miqdad_Jnr
Asali: Twitter

'Yan kasuwar Katsina za su samu tallafi

Mai ba Gwamna Dikko Umaru Radda shawara kan kafofin sada zumunta, Isah Miqdad ne ya sanar da hakan a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar Isah Miqdad ta ce an rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna a hukumance (MOU) a ranar Alhamis, 25 ga Janairu, 2024, a hedikwatar hukumar SMEDAN da ke Abuja.

Sanarwar ta kuma ce wadanda suka aiwatar da yarjejeniyar sun hada da Mista Charles Odii, shugaban SMEDAN, da Misis Aisha Aminu, shugabar hukumar KASEDA.

Yadda tsarin tallafin kudin zai kasance

Hadakar KASEDA da SMEDAN na daga cikin shirin 'MFP', wanda haɗin gwiwa ne tsakanin cibiyoyin kuɗi da jihar Katsina, da zai ba da lamuni ga 'yan kasuwa.

SMEDAN da gwamnatin jihar Katsina za su ba da gudunmawar Naira miliyan 500 kowanne domin aiwatar da shirin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi garkuwa da tsohon shugaban kungiyar NLC, an samu bayanai

A wannan zangon shekarar da aka shiga ne za a fitar da Naira miliyan 250 domin tallafawa kananun 'yan kasuwa kamar yadda sanarwar ta nuna.

Duba sanarwar a kasa:

Gwamnatin Katsina ta karbo bashi?

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin jihar Katsina ta ce rahoton hukumar kula da basussuka (DMO) na cewa Gwamna Dikko Radda ya karbo basussuka ba gaskiya bane.

Wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar ta ta kuma ce har yanzu yanzu gwamnatin APC mai ci a Katsina karkashin Gwamna Radda ba ta ciwo bashin ko kwabo ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.