Buhari Ya Sabunta Naɗin Umaru-Radda a Matsayin Shugaban SMEDAN

Buhari Ya Sabunta Naɗin Umaru-Radda a Matsayin Shugaban SMEDAN

- Shugaba Muhammadu Buhari ya sabunta nadin Dr Dikko Umaru-Radda a matsayin shugaban SMEDAN

- Sanarwar sabunta nadin radda ta fito ne daga ofishin sakataren gwamnatin tarayya, Mustapha Boss

- Umaru-Radda ya mika godiyarsa ga Shugaba Buhari da sauran yan Nigeria ya kuma yi alkawarin yi wa kasarsa hidima

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake nada Dr Dikko Umaru-Radda karo na biyu a matsayin shugaban Hukumar bunƙasa ƙanana da matsakaitan sana'o'i a Najeriya wato SMEDAN.

Sanarwar ta fito ne daga ofishin sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha a wata takarda mai dauke da kwanan watar 12 ga watan Maris na 2021.

Buhari Ya Sabunta Naɗin Umaru-Radda a Matsayin Shugaban SMEDAN
Buhari Ya Sabunta Naɗin Umaru-Radda a Matsayin Shugaban SMEDAN. Hoto: @daily_nigerian
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Matasan Arewa Sun Bawa Sunday Igboho Wa'adin Awa 72 Ya Kwashe Yarbawa Daga Arewa

Wasikar ta tabbatar da sake nadin Dr Dikko Radda a matsayin shugaban SMEDAN tare yi masa fatan alheri a wa'adinsa na biyu.

Mr Radda ya yi wa shugaban kasa godiya bisa sake bashi damar jagorancin hukumar da ya ce hakan ya faru ne bisa nasarorin da hukumar ta samu a karkashin wa'adinsa na farko.

Ya ce, "Dukkan godiya ta tabbata ga Allah, yau an sake sabunta nadi na a matsayin shugaban hukumar bunƙasa ƙanana da matsakaitan sana''o'i ta Nigeria, SMEDAN, na wasu shekaru biyar.

KU KARANTA: Samia Hassan: A Karon Farko, An Rantsar Da Mace Matsayin Shugabar Kasa a Tanzania

"Ina godiya bisa damar da aka bani na yi wa kasa ta hidima. Ina mika godiya ta ga Shugaba Muhammadu Buhari saboda amince wa da ya yi da ni wanda hakan ya bamu damar samun nasarori masu yawa a shekaru biyar da suka gabata.

"Ina godiya bisa goyon baya da na ke samu daga iyalai na, abokai da masu fatan alheri da sauran yan kasa. Nagode Allah ya muku albarka baki daya."

A wani rahoton daban kun ji cewa, rundunar yan sandan jihar Kano ta kwantar da jama'a hankula game da wasu bakin mutane tare da rakuma da suka bayyana a wasu sassan jihar.

Daily Nigerian ta gano cewa mazauna jihar sun ankarar da yan sanda kan bakin mutanen da suka yada zango a wasu sassan jihar.

Wasu mazauna garin suna zargin matafiyar sun iso jihar ne domin aikata laifi da sunan fataucin kanwa.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164