Sallamar ’Yan Fansho: Sarkin Kano Sanuni II Ya Aikawa Gwamna Abba Muhimmin Sako

Sallamar ’Yan Fansho: Sarkin Kano Sanuni II Ya Aikawa Gwamna Abba Muhimmin Sako

  • Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sha ruwan kalaman yabo kan kula da 'yan fansho da kuma inganta ilimin yara mata a Kano
  • Mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ne ya yi wannan yabon yayin da ya gana da wasu kwamishinonin Kano a fadarsa
  • Sarki Sanusi II ya kara da cewa gwamnati mai ci a Kano ta maida hankali ga ‘yan fansho da a baya aka jefa su cikin mawuyacin hali

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya yabawa Gwamna Abba Yusuf bisa kokarin da yake yi na magance matsalolin ‘yan fansho da maida hankali kan ilimin yara mata.

Kara karanta wannan

Shinkafi ya fadi abin da ke kawo rashin tsaro a Arewa maso Yamma, ya ba da mafita

Sarki Sanusi II ya kara da cewa gwamnati mai ci a Kano ta maida hankali ga ‘yan fansho da a baya aka jefa su cikin mawuyacin hali saboda rashin biyan su kudadensu.

Sarkin Kano ya yi magana kan 'yan fansho da ilimin yara mata
Sarkin Kano, Sanusi II ya yabawa Gwamna Abba Yusuf kan kula da 'yan fansho da ilimin mata. Hoto: @masarautarkano, @Kyusufabba
Asali: Facebook

Mai magana da yawun gwamnan jihar Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X a daren ranar Alhamis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sarki Sanusi II ya yabawa gwamnan Kano

Sanarwar ta ruwaito Sarki Sanusi II yana cewa:

“Bambancin da ke tsakanin kula da rashin kula wani lokacin tamkar bambanci ne tsakanin rayuwa da mutuwa ga mai karbar fansho ko danginsa.
"Wasu daga cikinsu sun mutu. Mu tuna cewa za mu tsayu a gaban Allah kan nauyin da ya rataya a wuyanmu ga wadanda suka yi wa jiharmu hidima tsawon shekaru 35."

Sarkin ya yabawa Gwamna Yusuf bisa kashe N6bn domin biyan kudin giratuti da na wadanda suka mutu da kuma karin N5bn domin ci gaba da biyan ma’aikatan da suka yi ritaya.

Kara karanta wannan

Muhammadu Sanusi II ya faɗi yadda za a magance matsalolin da suka addabi Najeriya

Gwamnatin Kano ta kula da ilimin mata

Sarkin Kano ya kuma nuna jin dadinsa da kokarin da Gwamna Abba Yusuf yake yi na inganta ilimin yara mata a jihar.

Sanusi II ya bayyana haka ne a lokacin da kwamishinan yada labarai na Kano, Baba Halilu Dantiye da takwaransa na kimiyya da fasaha, Mohammed Othman suka kai masa ziyara.

Ya jaddada cewa ilimin yara mata yana magance matsalolin da suka shafi auren wuri, kula da mata masu juna biyu, rashin abinci mai gina jiki da talauci, wadanda ya kamata a magance su.

Sanusi II ya magantu kan halin da ake ciki

A wani labarin, mun ruwaito cewa Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya magantu kan halin da Najeriya ke ciki da ma kokarin komawa tafarkin mulkin firaminista.

Sarki Sanusi II ya ce sauya tsarin mulki ba shi ne zai magance matsalolin Najeriya a halin da ake ciki ba, ya kuma zargi gwamnatin tarayya da katsalandan a harkokin jihohi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel