Ana samun ƙaruwar auren wuri saboda rashin inganta tsarin ilimi - Sarki Sanusi
Tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II, ya magantu a kan dalilin da ya sa ake samun ƙaruwar auren wuri a Arewacin Najeriya.
Sarki Sanusi ya ce babban dalilin da ya sa auren wuri ya ƙara tsananta a Arewacin kasar bai wuce rashin yi wa tsarin ilimi kyakkyawan tanadi ba.
Furucin hakan ya fito daga bakin tsohon Sarkin ne a wata hira da aka yi da shi a manhajar sadarwar zamani ta Zoom ta hanyar yanar gizo.
Sashen Hausa na BBC ya ruwaito cewa, Sarki Sanusi ya ce muddin ana son a shawo matsalar aure wuri, to kuwa ne sai an yi wa tsarin ilimi kyakkyawan tanadi ta hanyar inganta shi.
Ya ce hakan zai yiwu ta hanyar samar da makarantu da kuma wajabta neman ilimi a kan 'ya'ya mata.
Tsohon Gwamnan Babban Bankin kasar, ya ce gwamnatocin Najeriya ba su da ikon magance matsalar yi wa 'ya'ya mata auren wuri saboda duk sun sauka daga tafarkin inganta tsare-tsraen ilimi.
Ya tunatar da cewa har yanzu akwai dokar da ta haramtawa yi wa 'ya mace aure matukar ba ta kammala aji uku na makarantar sakandire ba.
Ya ce wannan doka tana nan a cikin kundin tsari na hukumar ilimin bai daya ta UBE, wadda ta shar'anta hukunta duk wani malami da aka kama ya daura auren macen da ba ta kammala aji uku ba.
"Amma babu wanda aka hukunta domin wanda ya kamata ya kai karar iyayen ba zai iya ba saboda bai samar da makarantun ba." inji shi.
"Tsohon sarkin na Kano ya ce muhawara ce ya kamata a yi."Mu tambayi kanmu kan shekarun da ya dace a aurar da 'ya mace"
KARANTA KUMA: Gwamna Ganduje ya yaba wa Gwamnatin Tarayya a kan inganta wutar lantarki a Kano
"Na zama sarki tare da sanin yadda tunanin mutanenmu na arewa yake yadda suke son aurar da 'yayansu."
"Kuma kasancewa ta sarki wanda ya fahimci gaskiyar yanayin talakawa, suna son ilmantar da 'ya'yansu amma babu makarantun."
Ya ci gaba da cewa, a wasu lokutan mahaifi zai tura 'yarsa makarantar firamare amma zai kasance ta je ta dawo ba tare da ta koyi komai ba, wanda hakan zai ga cewa babu wata riba a neman ilimin da ya tura ta.
"Ya kamata a ce sai yarinya ta kammala karatun sakandire kafin a yi mata aure." inji Sarki Sanusi.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng