“A Koma Salon Mulkinsu Sardauna”: An Fadawa Tinubu Hanyar Magance Matsalolin Najeriya
- An yi kira ga gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da ta koma amfani da salon mulkin shugabannin da suka karbowa Najeriya yanci
- Wata kungiya mai zaman kanta, NUP ta fadawa gwamnati cewa idan aka koma tsarin mulki n irinsu Sardauna, Najeriya za ta ci gaba
- Kungiyar NUP ta jaddada cewa har sai an kwaikwayi mulkin 'yan mazan jiya ne za a iya magance matsalolin tattali da na siyasa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - An bukaci gwamnatin tarayya da ta sake duba tsarin mulkin su Alhaji Abubakar Tafawa Balewa, Dr Nnamdi Azikiwe, Cif Obafemi Awolowo da Sir Ahmadu Bello.
An tabbatarwa gwamnatin cewa idan har ta koma amfani da salon mulkin magabata na kwarai, za ta shawo kan kalubalen tattalin arziki da siyasa da kasar ke fuskanta.
"A koma tsarinsu Sardauna" - NUP
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa shugaban kungiyar NUP na kasa, Ambasada Sixtus Obinna Nwoke da sakataren kungiyar, Saleh Alhassan Kubah ne suka yi wannan kiran.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sun yi wannan kiran ne a Abuja a wajen taron kaddamar da kwamitin gudanarwa na kungiyar (CWC) wanda ya samu halartar masana tattalin arziki daga sassan kasar.
Sun ce ba za a iya tsallake kalubalen da ake fuskanta a halin yanzu ba har sai an dauko tsarin salon mulki irin na shugabannin da suka samar da 'yancin kasar.
NUP ta tunatar da kokarinsu Sardauna
“Muna tunatar da kawunanmu da gwamnati irin namijin kokarin da magabatanmu na kwarai suka yi, wadanda suka sadaukar da rayuwarsu wajen ganin Najeriya ta samu ci gaba.
“Tsarin da suka bi wajen gudanar da mulki wani abin kira ne a gare mu da mu dora kan salonsu domin gina kasa mai cike da hadin kai, zaman lafiya da wadata.
“Dole ne mu hada kai a kokarinmu na samar da Najeriya wadda ta dace da tsarin irin kasar da muke so. Muna fatan Najeriya ta kasance kasar hadin kai, ‘yancin kai da kuma sadaukarwa."
- Ambasada Sixtus Obinna Nwoke.
Gwamnoni sun bada sirrin gyara tattali
A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnonin Najeriya sun ba gwamnatin Shugaba Bola Tinubu sirrin gyara tattalin arziki da kuma samar da abinci mai dorewa.
A wani jawabin bayan taro da kungiyar gwamnonin kasar suka fitar, sun ce ya zama wajibi tinubu ya magance matsalar tattalin arziki domin komai ya daidaita.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng