Hanyoyin rage radadin matsalar tattalin arziki a Najeriya

Hanyoyin rage radadin matsalar tattalin arziki a Najeriya

Hanyoyin rage radadin matsalar tattalin arziki a Najeriya

Shakka babu, kwanan nan ne aka tabbatar da cewa Najeriya ta samu durkushewar arziki. Kayan masarufi sun yi tsada. Jama’a na fama da yunwa a Najeriya. Ka san yadda za ka rage radadin wannan matsi?

Hanyoyin rage radadin matsalar tattalin arziki a Najeriya

 

 

 

Wata Kasuwa kenan a Najeriyar, a Birnin Legas.

Kasafi

A halin da ake ciki a Najeriya, dole sai mutum yayi kasafin yadda zai rika batar da kudin sa, kuma ta yadda ya dace. Mutum yayi lissafin abin da zai kashe shi kadai ko da iyalin sa, daga sutura har abinci. A kayyade abin da za a kashe bisa komi, hakan zai hana barna.

Abincin sayarwa

Dole mutum ya daina sayen abincin sayarwa, musamman masu tsada, dole a rage yawon kashe kudi kan abinci. Mutum ya fara sayen kayan abincin domin ya girka da kan sa. Kar a manta a sayi irin su Garri da gyada.

Adana

Sai kuma ana adana kudi a wannan yanayi. Don za a iya shiga lokutan da suka fi wannan tsanani, sai mutum ya fasa dan asusun sa. Domin kuwa za a dade a cikin wannan yanayi a Najeriya.

KU KARANTA: Za mu shawo kan matsalar tattalin arziki-Buhari

Rage Kashe kudi

A rage barna da kashe kudi babu gaira-babu dalili, kuma ba lokacin karbo bashi bane yanzu. Dole mutum ya rage kashe kudi a duk wani abu maras amfani, irin su; zuwa shakatawa, kallo a gidan wasa da dai sauransu.

Rage Ciki

Ya zama dole a duba, a rage ciki a wannan yanayi. Sai mutum yana aunawa yana ganin menene da kuma wanene ba ya bukata sosai a wannan marra. Kuma mutum ya kara dagewa wajen nema.

Saye da sayarwa

Akwai inda ake samun kaya cikin rahusa, sai mutum ya lakanci irin wadannan wurare idan har zai saye kaya. Hakan zai taimaka kwarai a wannan lokacin da ake fama a Najeriya. A wannan yanayi, zuwa kasuwa zai fi shiga shago amfani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng