Tattalin Arziki: Ba mafita illa a koma tsarin musulunci
– Masana sun ce mafita daga matsalar tattalin arzikin Najeriya shine a koma irin tsarin musulunci
– An bayyana haka ne a wani taron masana da aka gabatar a Garin Sokoto
– Dr. Ahmad Dogarawa na Jami’ar Ahmadu Bello ta Zaria yace idan aka yi amfani da tsarin musulunci za a samu sauki
Masana tsarin tattali na musulunci sun yi wani taro a Garin Sokoto domin bada shawarar yadda za a fita daga matsalar tattalin arzikin da aka shiga cika a Najeriya. Masanan sun yanke shawarar cewa babu wata mafita sai a koma irin tsarin musulunci idan har ana neman a kai ga ci ga matsalar tattalin arziki a Najeriya.
Bangaren Tattali na Jami’ar Usman Danfodio na Sokoto ya gudanar da wannan taro mai taken Matsalar tattalin Arziki a Najeriya; ta fuskar musulunci. Wanda ya gabatar da takarda a kan mau’du’in Dr. Ahmad Bello Dogarawa na sashen ilmin Akawu daga Jami’ar Ahmadu Bello ta Zaria yacr mafita na ga tsarin tattalin musulunci.
KU KARANTA: Matsalar Tattalin arziki; A komawa Coci inji Fasto Bakare
Dr. A. B Dogarawa yace idan har za ayi amfani da tsarin addinin musulunci a harkar tattalin arziki, lallai Kasar za ta fita daga matsalar da ta shiga. Daily Trust ta rahoto masanin yana kawo hadisai na Manzon Allah SAW, yana kiran Shugabanni su ji tsoron Allah a lamuran su.
Gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Tambuwal yace ba mamaki domin Kasashe kusan 75 na duniya na amfani da irin tsari musulunci.
Asali: Legit.ng