Matar Aure Ta Tsere Daga Hannun ’Yan Bindiga Yayin da Barci Yayi Awon Gaba da Miyagun
- Daya daga cikin matan aure uku da aka yi sace a wani kauyen Taraba makonni hudu da suka wuce ta tsero daga hannun 'yan bindigan
- An ruwaito cewa matar auren ta tsere daga hannun 'yan bindigar lokacin suna bacci, amma har yanzu sauran matan na tsare
- Mazauna garin Takum na fuskantar barazana daga 'yan bindiga da ke sace jama'a a kan hanyar Takum-Katsina-Ala
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jihar Taraba - Rahotanni sun bayyana cewa wata matar aure mai suna Amina Adamu ta tsere daga sansanin 'yan bindiga da suka yi garkuwa da su a lokacin da suke barci
An ruwaito cewa matar auren na daga cikin matan aure uku da aka sace su a hanyar Takum-Katsina-Ala a jihar Taraba makonni hudu da suka wuce.
Matar aure ta tsere daga wajen 'yan bindiga
A cewar jaridar Daily Trust, wani dan uwan mijin matar, Mallam Maiwada ne ya sanar da cewa Amina ta tsere daga hannun 'yan bindigar lokacin suna bacci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai Mallam Maiwada ya ce har yanzu akwai sauran matan aure biyu da diyar kanin Janar T.Y Danjuma a hannun masu garkuwa da mutanen.
An kuma tattaro cewa wasu mutane biyu da suka je kai kudin fansa domin a sako matan auren uku na hannun masu garkuwa da mutanen.
An yi garkuwa da kanin T.Y Danjuma
An yi garkuwa da dan uwan Janar T.Y Danjuma, Mista Benjamin tare da matarsa da diyarsa amma an sake shi bayan an biya kudin fansa.
Sai dai masu garkuwa da mutanen sun ki sakin matarsa da diyarsa.
'Yan bindiga sun addabi yankin Takum
Mazauna garin Takum na fuskantar barazana daga masu garkuwa da mutane da suke gudanar da ayyukansu ba dare ba rana a kan hanyar Takum-Katsina-Ala da Takum-Kashinbila.
Daya daga cikin mazauna garin Bello Haruna ya shaida wa manema labarai cewa akwai matukar hadari bi ta hanyoyin biyu saboda ayyukan masu garkuwa da mutane.
Mutane 3 sun tsere daga hannun 'yan bindiga
A wani labarin, mun ruwaito cewa mutane uku daga cikin mutane 11 da aka sace a kauyen Azzara a karamar hukumar Kachia, jihar Kaduna sun tsere daga hannun 'yan bindiga.
An ce mutanen uku sun samu nasarar tserewa ne bayan da 'yan bindigar suka sha giya suka bugu sannan bacci ya kwashe su, abin da ya ba mutanen kwarin guiwar sulalewa.
Asali: Legit.ng