Sa’o’i kadan bayan sace matan aure, ‘yan bindiga sun sake kai hari Birnin Gwari tare da sace wasu mutanen

Sa’o’i kadan bayan sace matan aure, ‘yan bindiga sun sake kai hari Birnin Gwari tare da sace wasu mutanen

Da sanyin safiyar yau ne wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da wasu matan aure uku a kauyen Maganda dake kan titin Birnin Gwari zuwa Funtua.

Sa’o’i kadan bayan faruwar hakan sai ga shi wasu ‘yan bindigar sun kara tare hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna inda suka kashe mutum daya tare da yin garkuwa da wasu 6.

Shugaban kungiyar direbobi ta NURTW a Birnin Gwari ya tabbatar da faruwar lamarin tare da bayyana cewar an samu gawar mutum daya day a mutu sakamakon yadda direban motar ya saki hanya domin kaucewa ‘yan bindigar.

Sa’o’i kadan bayan sace matan aure, ‘yan bindiga sun sake kai hari Birnin Gwari tare da sace wasu mutanen
Motocin jami'an tsaron Najeriya

Ko a asabar din wancan satin saida ‘yan bindiga suka tare hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna tare da yin garkuwa da wasu mutane 6 yayin da suke tafiya a cikin motar haya.

Lamarin harin ‘yan bindiga da yin garkuwa da mutane na kara ta’azzara a yankunan Arewa ta tsakiya da kuma Arewa ta yamma, musamman jihohin Kaduna da Zamfara.

DUBA WANNAN: Tura ta kai bango: Jama'a sun dakile wani harin kunar bakin wake da aka kai Masallaci a Yobe

A satin day a gabata ne wasu ‘yan bindiga suka sace tare da yiun garkuwa da wani injiniyan kamfanin gine-gine dan asalin kasar Syria tare da kasha jami’an ‘yan sanda uku a garin Sokoto.

Kimanin sati uku da suka wuce saida wasu ‘yan bindigar suka kai hari tare das ace wani injiniya dake aiki da wani kamfanin gina hanya a Sabontitin hanyar Madobi a birnin Kano.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng