'Yan Kasuwa Sun Faɗi Abin da Ya Jawo Tsadar Kayan Abinci, FCCPC Ta Kai Samame Onitsha
- 'Yan kasuwa sun shaidawa gwamnatin tarayya cewa tsadar kayan abinci ta samo asali ne daga matsalar rashin tsaro a kasar
- 'Yan kasuwar sun ce yanzu manoma sun daina fitar da kayan abinci da kansu saboda tsoron garkuwa daga 'yan bindiga
- Da muka tuntubi Abdulmunin Sani, wani dan kasuwa a jihar Kaduna, ya ce tsadar kayan abinci tana a ko ina, ba wai a kasuwa daya ba
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Awka, Anambra - Jami'an hukumar FCCPC sun kai samame babbar kasuwar kayan abinci ta Oseokwodo, Onitsha kan tsadar da kayan abincin suka yi.
Sai dai 'yan kasuwar sun shaidawa jami'an gwamnatin tarayyar cewa rashin tsaro a fadin kasar ne ya jawo hauhawar farashin kayan.
FCCPC ta kai samame kasuwar Onitsha
Jagoran shiyyar Kudu maso Gabas na hukumar FCCPC, Mista Jude Akonam ya ce sun kai samamen ne domin gano dalilin tsadar kayan, inji rahoton Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mista Akonam ya ce za su sanarwa hukumomin da ya dace abin da binciken su ya gano domin daukar matakin da ya dace kan tsadar abincin.
Tsadar abinci: 'Yan kasuwa sun magantu
Shugabannin 'yan kasuwar sun ce kasuwar Oseokwodo ta kasance wuri da jama'a ke sayen kayan abinci a cikin farashi mai rahusa.
Amma sun ce tashin farashin kayan abinci a kasuwar alama ce da ke nuni da cewa lamarin ya fi karfin 'yan kasuwar ne su ma.
Sakataren kungiyar OOMTU, Mista Onyekekwe Cyprian wanda ya bayyana kasuwar matsayin cibiyar hada-hadar kayan abinci ya Anambra, ya ce tsadar ba daga su bane.
"Matsalar tsaro ne silar tsadar abinci" - Cyprian
Da yake alakanta lamarin ga matsalar tsaro, Mista Cyprian ya ce yanzu manoma na tsoron zuwa gonakinsu saboda 'yan bindiga da ke sace su, jaridar The Punch ta ruwaito.
Shugaban 'yan kasuwar ya ce sau tari ana tare manoma a gona ko a hanyar zuwa kai kaya kasuwa ko a hanyar dawowa ayi garkuwa da su.
Ya ce wannan dalilin ya sa yanzu kayan abinci ya yi ƙaranci a kasuwa, yayin da su 'yan kasuwar ne ke zuwa wajen manoman da kansu suna dauko kayan.
"Tsadar kayayyaki ma ko ina" - Dan kasuwa
Da muka tuntubi Abdulmunin Sani, wani dan kasuwa a Kasuwar Bacci, jihar Kaduna, kan farashin kayan abinci, ya ce tsadar kayan abinci tana a ko ina, ba wai a kasuwa daya ba.
Malam Abdulmunin Sani ya bayyana cewa kayan abincin da suka gaza yin sauki a Arewa dole ne su yi tsada a Kudu tunda kai masu ake yi.
A yau Juma'a, ɗan kasuwar ya ce ana sayar da buhun shinkafa 'yar gida N72,000 har zuwa N75,000 ya danganta da kamfanin da mutum ke so.
Katan ɗin taliya kuwa yana nan a kan N16,300 yayin da Malama Abdulmunin ya ce ba kasafai ne jama'a ke sayan kayan abinci 'yan kasar waje ba, kuma ba ko ina ake samunta ba.
Dan Kasuwar ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta samar da matakan da za su taimaka wajen ganin manoma sun yi wadataccen noma a wannan shekarar.
'Yan kasuwar Kano sun karya farashin abinci
A wani labarin, mun ruwaito cewa 'yan kasuwar hatsi na jihar Kano sun karya farashin kayan abinci sakamakon tsadar rayuwa da ake fuskanta a kasar.
Shugabannin kasuwar sun koka kan yadda kayan abincin ke tsada yayin da kuma ciniki yayi karanci a kasuwannin saboda rashin kuɗi a hannun jama'a.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng