WHO: Adadin Mutanen da Ke Mutuwa a Shekara Saboda Shan Barasa Ya Kai Miliyan 2.6
- Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce aƙalla mutane miliyan 2.6 ne ke mutuwa daga shan barasa a kowacce shekara a fadin duniya
- Daga cikin wannan adadin, rahoton ya ce mutane miliyan 2 maza ne, kuma suna hadawa da shan sauran miyagun kwayoyi da ke kisa
- Bisa ga alƙaluman 2019 da WHO ta tattaro, mutane miliyan 1.6 sun mutu daga cututtuka da suka hada da kansa ta dalilin shan giya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Rahoton da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta fitar a ranar Talata ya nuna cewa aƙalla mutane miliyan uku ke mutuwa kowace shekara sanadiyyar kwankwaɗar barasa.
Hukumar WHO, wanda ke aiki karkashin Majalisar Dinkin Duniya (UN) ta ce mashayan giya na mutuwa ta hanyar tuki, cin zarafi, cututtuka da sauransu.
Mashayan giya 2.6m suka mutu a 2019
Rahoton da aka wallafa a shafin WHO, ya ce mashayan giya miliyan 2.6 suka mutu a 2019, wanda ke wakiltar kashi 4.7 na adadin mutanen da suka mutu a duniya a shekarar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yayin da rahoton ya nuna cewa ana samun rayuwar mashayan giya da ke mutuwa a shekara-shekara, ya ce maza ne ke da kaso mafi tsoka a mace-macen.
Mafi yawan lokacin da mashayan giya suka mutu a duniya shi ne a shekarar 2019, kuma 'yan shekara 20 zuwa 39 ne suka fi mutuwa, in ji rahoton WHO.
Me yake jawo mutuwar mashayan giya?
Kansa da hatsarin mota
Hukumar lafiyar ta ce shan giya yana haddasa cututtuka ga ɗan Adam, da suka haɗa da cutar hanta da kuma kansa.
A rahoton 2019, mutane miliyan 1.6 suka mutu daga cututtuka da suka hada da, kansa, hatsarin mota, cututtukan hanta, duka kuma sanadin shan giya.
Mutanen turai ne suka fi shan giya, sai Amurka da ke bin bayanta. Mafi ƙarancin shan giya ita ce Arewacin Afrika, inda Musulmi suka fi yawa.
Masu yawan shan giya
Daga cikin mutanen da suke shan giya a 2019, rahoton WHO ya nuna cewa akwai rikakku a harkar masu shan karanci giram 27 na giya kullum.
Rahoton ya kuma nuna cewa kashi 23.5 na masu maitar shan giya 'yan shekara 15 ne zuwa 19, wanda ke wakiltar kaso 45% a Turai, da kaso 44% a Amurka.
NELFund ta dauki mataki kan jami'o'in jihohi
A wani labarin kuma, mun ruwaito cewa hukumar da ke kula da asusun ba da rancen karatu (NELFund) ta rufe ba da rancen ga ɗaliban manyan makarantun jihohi.
Hukumar NELFund ta ce ta dakatar da daliban daga neman rancen kudin har sai makarantun sun kammala dora bayanan dalibansu domin tantancewa nan da farkon Yulin 2024.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng