Dan shekaru 48 ya rasu bayan lashe gasar shan giya

Dan shekaru 48 ya rasu bayan lashe gasar shan giya

Wani mutum mai shekaru 48 dake zaune a yankin Kamudili, a gabashin kasar Uganda ya mutu a ranar lahadi 7 ga watan agusta bayan ya lashe gasar shan giya a ranar Asabar.

Dan shekaru 48 ya rasu bayan lashe gasar shan giya

Jaridar Edaily ta ruwaito an tsinci gawar mamacin ne a gefen hanya kusa da mahadar da aka gudanar da gasar. A cewar majiyar gani da ido, mutumin ya rasu ne bayan ya sha giya da ta wuce misali a yayin gasar.

Mutumin ya sha giya ne da ta mai katutu a cikin kokarinsa na cinye gasar ba tare da ya lura da illar abin ba. Jama’an garin sun koka da yawan mutuwar dake afkuwa daga illar shan giya. A wani labarin kuma, shugaban kasar Tanzania John Magufuli ya sallami minstan al’amuran cikin gida na kasar Charles Kitwanga akan laifin zuwa majalisa cikin maye. Kamar yadda mai magana da yawun shugaban kasar ya fadi yace, an sallami Kitwanga ne saboda rashin da’a. sallamar nasa ya biyo ne bayan ya mika kasafin kudin ma’aikatan sa kenan na shekarar 2016/2017.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng