Najeriya ce kasa ta 1 da aka fi kwankwadar barasa a nahiyar Afrika

Najeriya ce kasa ta 1 da aka fi kwankwadar barasa a nahiyar Afrika

-Yawaitar mashaya a kowanne wajen zama a kudanci kasar nan ne ya tabbatar da wannan rahoton gaskiya ne.

- Kasar Najeriya ce ta kasance ta kan gaba a nahiyar Afirka ta kan gaba a yawan mashaya giya ko barasa

- A halin yanzu, akwai kamfanonin sarrafa giya akalla takwas a Najeriya kuma da yawansu na Kudancin kasar nan ne

A wani rahoton da ya fita cikin kwanakin nan, kungiyar masu binciken kasuwa ne suka jagoranci hakan.

Kamar yadda rahoton ya bayyana, shan giya a Afirka anyi kiyasin ya kai kashi 5 a hauhawa tsakanin 2015 zuwa 2020. Wannan ne mafi yawa a nahiyoyin duniya baki daya.

A nahiyar Asia, shan giya ya kai kashi uku, inda gabas ta tsakiya da Afirka ta Arewa ke da kashi 2.8 sannan Yammacin Turai ke da kashi daya, kamar yadda jaridar Within Nigeria ta gano.

A nahiyar Afirka kuwa, Najeriya ce ke kan gaba a sahun kasashe 10 da aka fi dirkar giya. Wannan kuwa za a iya cewa yana da nasaba ne da yawan ‘yan Najeriya wanda ya tumbatsa ya fi kowacce kasa a Afirka.

Wannan rahoton na bayyana cewa giya ta mamaye kashi 16 na abinda ake sha a Najeriya inda sauran launin lemuka suka kwashe kashi 84.

KU KARANTA: Mijin tace: Mata za ta yiwa mijinta saki uku saboda ya nemi irin aikin da take nema

A nahiyar Afirka, kasar Uganda ce take biye da Najeriya wacce ke da kashi 11.93, sai kasar Botswana wacce ke da kashi 7.96 da kuma kasar Kenya wacce ta zo a ta hudu kuma tana da kashi 7.92.

Kamar yadda wani bincike da wani kamfanin kasuwanci na Najeriya ya gudanar a watan Nuwamba na 2015, an gano cewa ana samun yawan shan giya a ‘yan Najeriya. Amma kuma rahoton ya nuna cewa, masu shan giyar na Najeriya suna komawa shan jikon gargajiya ne.

Wannan yayin kuwa shi ne ya kawo maganar magungunan gargajiya masu kunshe da giya kamar su Alomo Bitters, Origin Zero da kuma Origin tare da sauran magungunan gargajiya.

A halin yanzu, akwai kamfanonin sarrafa giya guda takwas a Najeriya kuma yawancin wadannan kamfanonin na Kudancin Najeriya ne.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel