Ana Dambarwar Masarauta, Abba Ya Jajubo Ayyuka 25, Katangar Sarki Za Ta Ci N99m

Ana Dambarwar Masarauta, Abba Ya Jajubo Ayyuka 25, Katangar Sarki Za Ta Ci N99m

  • Majalisar zartarwa ta jihar Kano tayi zama a karshen makon nan, an amince da wasu manyan ayyuka
  • Gwamnatin Abba Kabir Yusuf za ta gyara katangar gidan Sarki a Nasarrawa kuma za a yi aiki a makarantu
  • Gyara da ginin cibiyar kula da masu cutar sikila a asibitin kwararru na Murtala Muhammad zai ci ₦81,621,546

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kano - A lokacin da ake ta hayaniya a dalilin shari’ar masarauta a jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya jagoranci zaman majalisar SEC.

Majalisar zartarwa ta jihar Kano tayi zama a karkashin Mai girma Abba Kabir Yusuf a ranar Asabar inda aka amince da wasu ayyuka.

Abba Kabir Yusuf
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da ayyukan N8bn a Kano Hoto: @KyusufAbba
Asali: Twitter

Abba Kabir Yusuf ya yi zaman SEC

Kara karanta wannan

'Aminu Ado Bayero a makabarta yake zaune ba fadar Sarki ba' Inji Gwamnatin Abba

Kamar yadda Abba Kabir Yusuf ya sanar a shafinsa na Facebook, wannan shi ne zaman majalisar zartarwar na 15 a gwamnatinsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abba Yusuf ya amince da aikin gyara da kuma gina sashen masu cutar sikila a asibitin kwararru na Murtala Muhammad a Kano.

Za a samar da karin malaman asibiti

Gwamnan ya ce yana mai farin cikin sanar da ya yi na’am da kwangilar gina babbar makarantar koyon aikin ungonzoma a Gezawa.

Gwamnatin Abba za ta karasa gina makarantar koyon aikin jinya a karamar hukumar Madobi wanda zai ci N57,066,422.52.

Katangar gidan Sarkin Kano ta ci N99m

Muaz Magaji wanda ya yi kwamishina ya jawo hankalin jama’a a Facebook cewa za a gina katangar gidan sarki a Nasarawa kan N99m.

Dama can gwamnatin Kano ta sanar da cewa tana kokarin gyara ginin da Aminu Ado Bayero yake ciki tun a karshen watan Mayu.

Kara karanta wannan

‘Burgar banza’: Hadimin Ganduje ya takalo Abba kan yunkurin fatattakar Sarki Aminu

Kano: Sauran ayyukan da Abba ya amince

Sauran ayyukan da za a yi sun hada da samar da ruwa a wasu garuruwan Kano a yanzu da al'umma ke kukan karancin ruwan sha.

Har ila yau, an amince a biya ma’aikatan jami’ar Aliko Dangote da na Maitama Sule N447,621,640.79 a matsayin kudin karin wahala.

Gyaran makarantu da asibitoci, kotu da ofisoshi yana cikin ayyukan da gwamnan da mukarrabansa suka amince da su a zaman jiya.

Jimillar kudin da za a batar wajen wadannan ayyuka a Kano ya kai N8,629,636,749.4964.

"Aminu Ado ya tare a makabarta" - Abba

Ana da labari cewa Gwamnatin Kano ta ce saboda darajar Aminu Ado Bayero ake so a gyara gidan Nassarawa domin ya sukurkuce.

Abba Kabir Yusuf ya ce Sarkin Kano na 15 ya tare ne a makabartar da ake birne sarakuna daga ciki har da mahaifinsa, Ado Bayero.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng