"Yadda Abba Yayi Abin da ba a Taba Gani ba a Tarihin Jihar Kano" Inji Hadimin Gwamna

"Yadda Abba Yayi Abin da ba a Taba Gani ba a Tarihin Jihar Kano" Inji Hadimin Gwamna

  • Malam Hassan Sani Tukur ya ce kasafin kudin Kano na shekarar 2024 ya shiga tarihi, ba a taba ganin irinsa ba
  • Mai taimakawa gwamnan Kano wajen harkokin sadarwa ta yanar gizo ya yabi kason da aka warewa ilmi
  • Abba Kabir Yusuf zai kashe kusan 30% domin inganta ilmi, Hassan Tukur ya yiwa Legit bayanin tasirin hakan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Kano - Hassan Sani Tukur ya zanta da jaridar Legit inda mu ka tattauna da shi game da wasu manufofin gwamna Abba Kabir Yusuf.

Malam Hassan Sani Tukur babban mai taimakawa gwamnan Kano ne a harkokin sadarwa na zamani, a shekarar bara aka nada shi.

Gwamnan Kano
Gwamnan Kano ya warewa ilmi 29% a kasafin kudin bana Hoto: budget.kn.gov.ng
Asali: UGC

Meysasa Abba ya damu da ilmi

Hadimin gwamnan ya bayyana mana cewa a gwamnatinsu ta Kwankwasiyya, babu abin da suka sa a gaba kamar harkar ilmi.

Kara karanta wannan

Rikicin sarauta: Gwamna Abba na cikin Matsala, an bayyana sahihin Sarkin Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, sun lura babu abin da yake maida maras shi ya zama mai shi, talaka ya zama mai hali kamar samun ilmi na zamani.

"Mu a wurinmu harka ta ilmi ita ce ta daya, ta biyu kuma ta uku."
"Dalili kuwa mu na da fahimta cewa ta hanyar ilmi ne wanda ba ‘dan kowa ba zai taka ya zama wani."

- Hassan Sani Tukur

Kasafin kudi: Ilmi ya samu 29% a Kano

Saboda haka ya ce gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta ware 29% ga ilmi a kasafin kudin 2024 kamar yadda jaridar Vanguard ta kawo.

A hirarmu da shi, Tukur ya ce wannan kudi wanda ya kai N120bn zai taimaka sosai wajen dawo da martaba da kimar ilmi a Kano.

UNESCO ta na ba da shawarar a rika kashe akalla 15% domin ilmi a Najeriya, Premium Times ta taba yin bincike kan haka.

Kara karanta wannan

Abin da ya tada hankalin Abba Gida Gida bayan shiga ofis Inji Hadimin Gwamna

Yadda Abba zai farfado da ilmin Kano

Daga makudan kudin da aka ware za a gyara aji tare da gina wasu sababbi a makarantun firamare da sakandaren gwamnati a jihar.

Hassan ya ce gwamnatinsu za ta samar da kujeru domin jin dadin daukar karatu a Kano, wannan kokari zai shafi aji kimanin 29, 000.

Gwamnatin Kano ta waiwayi malaman makaranta

A bangaren jin dadi da kula da malamai, an kawo tsaarin da za a rika ba su bashin kudi a yanzu da ake cikin matsin tattalin arziki.

Akwai malaman BESDA da aka ba aikin gwamnati kuma za a sake daukar wasu.

Hadimin gwamna yace da gaske ake yi

“Wadannan tsare-tsare ne da za a yi su, kuma za a ba su muhimmanci sosai domin a yi gaggawar magance kalubalen nan.”
“Abin da wannan yake nufi shi ne, za a kula da dawainiyar malamai, ginin makarantu, kayan aiki da kayan ‘yan makaranta.”

Kara karanta wannan

‘Burgar banza’: Hadimin Ganduje ya takalo Abba kan yunkurin fatattakar Sarki Aminu

Gwamna Abba da dokar ta ba-ci a ilmi

A baya an ji cewa shekara guda bayan shiga ofis, Mai girma gwamnan Kano ya ayyana dokar ta-baci domin gyara harkar ilmi.

Abba Kabir Yusuf ya yi alkawarin cew zai kokarin bunkasa ilmi a lokacin da yake kokarin zama gwamnan jihar Kano a zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng